'Yan Najeriya sun fadi ra'ayoyinsu kan karin harajin VAT da gwamnati ke shirin yi

'Yan Najeriya sun fadi ra'ayoyinsu kan karin harajin VAT da gwamnati ke shirin yi

'Yan Najeriya da dama sun tofa albarkacin bakinsu kan shirin karin harajin kayyaki VAT daga kashi 5 zuwa kashi 7.2 cikin 100 inda mafi yawancin su suka nuna rashin jin dadin su kan shirin karin harajin.

Ministan Kudi da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed ne ta bayyana shirin karin harajin a karshen taron Majalisar Zartarwa na Kasa (FEC) da aka gudanar a ranar Laraba 11 ga watan Satumba kamar yadda Legi.ng ta ruwaito.

Ministan ta ce an nemi majalisar ta amince da karin harajin ne zuwa 7.2% domin gwamnatin tarayya tana amfani da kashi 15 cikin 100 na harajin ne kacal yayin da kashi 85 cikin 100 yana zuwa ne wurin gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi domin su kara kan harajin da suke karba su samu damar sauke dauyin jama'a da ke kansu.

Ministar ta ce FEC ta bayar da umarni fara tuntubar gwamnotocin jihohi da kananan hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki kafin sabon tsarin ya fara aiki a cikin shekarar 2020.

DUBA WANNAN: Wani mutum da ya yi sojan gona a matsayin CP ya damfari sanatan arewa N1.8m

Ministan ta kuma ce karin harajin zai taimakawa gwamnoni samun ikon biyan sabon albashi mafi karanci.

Ga dai abubuwan da wasu 'yan Najeriya suka fadi kan harajin a shafin Twitter.

Sanata Shehu Sani ya yi hasashen cewa ba za a bata lokaci ba wurin aiwatar da harajin kamar yadda aka ta jan kafa kan batun karin albashi mafi karanci.

Dakta Joe Abah ya ce Najeriya tana daga cikin kasashe mafi karancin VAT amma yana ganin ba wannan lokacin ya kamata ayi karin ba duba da cewa 'yan Najeriya suna cikin mawuyacin hali. Ya ce kamata ya yi a sanya harajin kan kayayaki masu tsada amma banda kayan masarufi da talakawa ke amfani da shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel