Mama Taraba ta sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP

Mama Taraba ta sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP

- Aisha Jummai Alhassan ta sauya sheka daga jam'iyyar UDP zuwa PDP

- Tsohuwar ministan harkokin mata ta yi takarar kujerar gwamnan jihar Taraba a tsohuwar jam'iyyarta ta UDP

- Jummai ta sake jaddada goyon baya ga Atiku Abubakar wanda ta bayyana shi a matsayin ubangidanta

Tsohuwar ministan mata ta Najeriya, Aisha Jummai Alhassan, wadda aka fi sani da Mama Taraba, ta sauya sheka daga jam'iyyar UDP zuwa babbar jam'iyyar hamayya a kasar ta PDP.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Mama Taraba ta bayyana ra'ayin hakan ne a yayin taron masu ruwa da tsaki na tsohuwar jam'iyyarta, UDP, (United Democratic Party).

Hakika Mama Taraba ta kasance tsohuwar minista a wa'adin farko na gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a karkashin inuwa ta jam'iyya mai ci ta APC.

Tun a yayin babban taron da aka gudanar bayan kammala babban zaben kasa na 2019, da yawa daga cikin mambobin jam'iyyar UDP reshen jihar Taraba, sun yanke shawarar sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa ta PDP.

KARANTA KUMA: 'Yan daban daji sun sako mutane 30 da suka yi garkuwa da su a jihar Katsina

A cewarta, ba ta da wani zabi a yanzu face karbar hukuncin da mafi rinjayen kaso na jam'iyyar wajen sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP.

Ana iya tuna cewa, an cece-kuce biyo bayan bayyanar wani faifan biyo wanda Mama Taraba tayi ikrarin goyon bayan takarar shugabancin kasa ta Atiku Abubakar duk da kasancewarta minista a gwamnatin Buhari.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel