IRT sun kama gagararren jagoran yan bindiga da ya sace mutane 50 a Kaduna

IRT sun kama gagararren jagoran yan bindiga da ya sace mutane 50 a Kaduna

Jaruman rundunar Yansandan Najeriya na musamman dake karkashin umarnin babban sufetan Yansandan Najeriya, Muhammad Adamu, IRT, sun samu nasarar kama wani kasurgumin mai garkuwa da mutane a jahar Kaduna.

Wannan mugun mutumi sunansa Bello Audu ana yi masa inkiya da Yellow ya bayyana cewa shi da kansa ya yi garkuwa da sama da mutane 50 a kan babbar titin Kaduna zuwa Abuja, kuma ya kashe sama da mutane 10.

KU KARANTA: Karya doka: An yi won gaba da shahararren mawaki Naziru Ahmad

Bello ya bayyana haka ne yayin da yake tattaunawa da DSP Aliyu Muhammad Auwal, guda daga cikin jami’ar Yansandan IRT dake karkashin jagorancin DCP Abba Kyari, inda ya shaida masa cewa shekarunsa 40 a rayuwa, kuma sana’arsa sata.

Yellow yace shi dan asalin garin Kajuru ne a jahar Kaduna, amma ya koma garin Kara dake yamma da mokwa a jahar Neja, Inda ya kara da cewa yana da mata 2 kuma yana da yara guda 5.

A jawabinsa, Yellow yace a cikin mutanen da suka yi garkuwa dasu, akwai inda suka amshi naira miliyan uku uku har sau shida, sa’annan a wasu lokutta sun amshi naira miliyan 10, miliyan 17, miliyan 16, miliyan 19, da kuma miliyan 20 a matsayin kudaden fansa.

Bello ya ambaci sunayen abokan aikinsa kuma manya a harkar garkuwa da mutane da suke da yara a karkashinsu kamar su Razak, Kachalla Nasiru, Shade, Baba, Gade, Taurari, Garsu da kuma Kishshi, sa’annan yace suna amfani da bindigar AK 47

“Ni dai ina sayen bindigogi na a hannun Yau, yaron Alhaji Duro dan asalin garin Kajuru, muna sayen AK akan kudi N600,000 zuwa N650,000 har zuwa N700,000, kuma ina sayen kwantena na harsashi, akan duk guda daya N1000.” Inji shi.

Daga karshe yace ya saci shanu sama da guda dubu dari, kamar yadda Legit.ng ya ruwaito shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel