Takaicin duniya ya sa wani dan shekara 27 rataye kansa a Kano

Takaicin duniya ya sa wani dan shekara 27 rataye kansa a Kano

Wani matashi, Nasiru Aliyu Abdussalam, na kwatas di Shekar Maidaki, karamar hukumr Kmbotso na jihar Kano, ya rataye kansa har lahira kan wani dalili da ba a sani ba.

An tsici gawar Nasiru mai shekara 27, rataye a saman rufin dakinsa, lokacin da abokan kasuwancinsa suka so karban odar wasu bulon gini da suka bashi.

Wasu rahotanni sun yi zargin cewa marigayi Nasiru ya rataye kansa ne saboda yana ta kokarin yin aure shekaru da dama amma mahaifiyarsa tana ta buwayar kokarinsa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, mahaifiyar marigayin, Malama Amina Umar Ahmad, ta bayyana cewa yan kwanaki kafin mutuwarsa, Nasiru ya kasance dauke da damuwaa fuskarshi har ta kaisa ga cewa “duk wanda ya mutu yanzu ya huta da wahalar wannan rayuwa.”

Tace kimanin shekaru shida da suka gabata, an gano cewa marigayi Nasiru na fama da kunci da damuwa a asibitin kyarwa na Aminu Kano.

Tace lamarin ya kai har Nasiru baya shan maganinsa sai da ta dunga nikawa sannan zuba masa a abincinsa. Mahaifiyar tasa tace harta yanke shawarar komawa asibiti domin mayar da maganin zuwa allura a matsayin maganin gyambon ciki.

Malama Amina ta alakanta damuwar da marigayi Nasiru ya shiga zuwa ga shekara 13 da suka gabaa lokacin da mijinta ya sake ta sannan ta tafi da yaranta ciki harda marigayi Nasiru. Tayi zargin cewa mahaifinsa ya yanke shawarar korarsa saboda ya zabi zama da mahaifiyarsa.

Wani makwabci kuma abokin marigayin, Hassan Sulaiman Adam, ya bayyana cewa suna tare tsawon shekara bakwai inda anan ya lura Nasiru na tattare da damuwa amma baya son sanar da kowa abunda ya shafi gidansu.

Sulaiman yace ba a yiwa mahaifiyar Nasiru adalci ba idan har aka daura laifin mutuwarsa a kanta.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa na jefa dan cikina mai watanni 4 a rafi - Aliyu

Mutane da dama sun yi juyayi akan lamarin, inda suka bayyana Nasiru a matsayin mai hakuri da ba a taba tunanin zai iya halaka kansa ba.

Da aka tuntubi kakakin yan sandan Kano, ASP Abdullahi Haruna, ya tabbatar da lamarin, yace kwamishinan yan sandan jihar yayi umurnin yin bincike da kyau a kan mutuwarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel