Kotun zabe: Gwamna Dapo Abiodun da Adekunle Akinlade za su san makomarsu ranar Asabar

Kotun zabe: Gwamna Dapo Abiodun da Adekunle Akinlade za su san makomarsu ranar Asabar

- Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun da dan takarar shugabancin jihar a karkashin jam'iyyar APM, Adekunle Akinlade zasu san sakamakon shari'arsu

- Dan takarar shugabancin jihar karkashin jam'iyyar APM, Adekunle Akinlade ne ya garzaya kotun ya kai korafin

- Kotun ta tabbatar da cewa a ranar asabar mai zuwa wanda ya yi daidai da 14 ga watan Satumba ne kotun zata sanar da hukuncin da ta yanke

A ranar Asabar ne gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun; da dan takarar kujerar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar APM, Adekunle Akinlade za su san makomarsu.

A yau Talata ne kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar ta bayyana cewa ta shirta tsaf don bayyana sakamakon karar da Akinlade ya kai na kalubalantar nasarar Abiodun na jam'iyyar APC.

DUBA WANNAN: Jam'iyyar APC ta dau alwashin daukaka kara akan nasarar da kotu ta baiwa Ekweremadu

Majiyarmu ta gano cewa kotun ta bada sanarwar cewa a ranar asabar 14 ga watan Satumba, 2019 zata sanar da hukuncinta.

Takardar sanarwar da sakatariyar kotun sauraron kararrakin zaben ta sa hannu itace kamar haka, "Hukuncin karar zaben za a ji ta ne a babbar kotun a ranar asabar, 14 ga watan Satumba, 2019."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel