Tattakin Ashura: Yan Shia sun sake yin artabu da Yansandan Najeriya a Bauchi

Tattakin Ashura: Yan Shia sun sake yin artabu da Yansandan Najeriya a Bauchi

Hankula sun tashi, jama’a sun shiga dimuwa yayin da wasu ayarin yan shia suka yi gaba da gaba da jami’an rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Bauchi a garin Bauchi a ranar Talata, 10 ga watan Satumba, inji rahoton Punch.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito lamarin ya auku ne da misalin karfe 10 na safiyar Talata a daidai shatale talen babbar kasuwar garin Bauchi da kuma Tashan Babiye, duk a cikin garin Bauchi.

KU KARANTA: Ina neman Bilkisu ta bani y’ay’ana 3 tun da ta sake aure – Hassan ya roki kotu

Yan sun fito ne da nufin gudanar da tattaki na tunawa da kuma nuna juyayin mutuwar Imam Hussaini ibn Ali, wanda aka kashe a yayin yakin Karbala shekaru fiye da dubu daya da suka gabata, kamar yadda suka saba a ranar 10 ga watan Muharram.

Rahoton ya tabbatar da cewa Yansanda sun yi harbe harben barkonon tsohuwa da kuma alburusai wajen tarwatsa dandazon yan shi’an, wanda hakan yasa jama’a kowa ya yi ta kansa, aka kulkulle shaguna.

Sai dai babu rahoton samun koda mutum daya da ya mutu, amma shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa mutane da dama sun samu na’o’in rauni daban daban.

A wani rahoto, rundanar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Kano, ta jibge fiye da jami'ai 200 a cikin birnin Kanon Dabo domin hana tattakin 'yan kungiyar shi'a, lamarin da ta ce ba za ta bari a gudanar da duk wani abu mai barazana ga zaman lafiya a kasar ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel