Mabiya Shia'a fiye da 30 sun mutu sakamakon 'turereniya' yayin tattaki a 'Karbala'

Mabiya Shia'a fiye da 30 sun mutu sakamakon 'turereniya' yayin tattaki a 'Karbala'

A kalla mabiya Shi'a 30 ne suka mutu a ranar Talata sakamakon wata turereniya a wata cibiyar bauta dake birnin Karbala a kasar Iraqi yayin da suke tuna wa da ranar 'Ashoura'.

Fiye da wasu mutane 100 sun samu raunuka a wurin mai nisan kilomita 100 a gabashin babban birnin kasar Iraqi, Baghdad.

Jami'i a ma'aikatar lafiya ta kasar Iraq, Saif al-Badr, ya ce adadin mutanen da suka mutu da wadanda suka samu rauni zai iya karu wa.

Turereniyar ta kasance mafi muni a tarihin tuna wa da ranar Ashoura da mabiya Shi'a ke yi.

Lamarin ya faru ne bayan masu tattakin sun firgita sakamakon karyewar wata gada da suke bi ta kai.

Mabiya Shi'a daga sassan duniya kan cika makil a Karbala duk shekara domin tuna wa da mutuwar Hussein, jikan annabi Muhammadu.

Kisan Hussein da mabiya Khalifa Yazid suka yi a shekarar 680, shine musabbabin rabuwar kai tsakanin mabiya Shi'a da Sunni a cikin addinin Islama.

Mabiya Shi'a a Iraq, Iran, Pakistan, Afghanistan, India, da Lebanon na tuna wa da ranar ta hanyar gudanar da tattaki, addu'o'i da kula raunata jikinsu.

Haka mabiya Shi'ar ke gudanar da tattaki duk shekara a nan gida Najeriya domin tuna wa da ranar Ashoura.

Sai dai, hukumar 'yan sandan Najeriya ta haramta kungiyar Shi'a, wacce ke kiran kan ta da IMN (Islamic Movement in Nigeria), biyo bayan tirjiyarsu da kuma rashin girmama dokokin kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel