Ashura: Mun gano makarkashiyar da gwamnati ta shirya mana - 'Yan Shi'a

Ashura: Mun gano makarkashiyar da gwamnati ta shirya mana - 'Yan Shi'a

Kungiyar Islamic Movement In Nigeria (IMN) ta yi ikirarin cewa ta gano shirin da Gwamnatin Tarayya tayi na kashe wasu mutane yayin tattaki na Ashura da za suyi a Abuja da sauran biranen Arewacin Najeriya a ranar Talata domin a ce 'yan kungiyar ne suka kashe mutanen.

The Punch ta ruwaito cewa kungiyar da aka fi sani da Shi'a ta ce ta gano cewa 'Yan sanda za su kai musu hari tare da kama ko wani kashe duk wani da aka samu yana tattakin na Ashura.

Wani mamban kungiyar ta IMN, Abdullahi Musa da ya yi wannan zargin a ranar Litinin ya yi kira ga shugabanin addini da kungiyoyin kare hakkin al'umma da kasashen ketare su sanya ido kan yadda tattakin zai kasance don tona asirin wadanda ke son tayar da fitina.

Ashura dai biki ne na addini da 'Yan Shi'a suke yi a duk fadin duniya.

DUBA WANNAN: Sabbin ministoci 5 da ke da 'jan aiki' a gabansu

A wata sanarwar da shugaban sashin watsa labarai na kungiyar, Ibrahim Musa ya fitar a ranar Litinin, ya yi ikirarin cewa Gwamnatin Tarayya 'tana shirin kashe jami'an tsaro, 'yan jarida da wasu mutanen sannan su ce 'yan kungiyar ne suka aikata kamar yadda su kayi a watan Yuli a Abuja'.

Sanarwar ta kara da cewa, 'Muna kira ga jami'an tsaro da 'yan jarida da mutane su sanya ido. Saboda haka al'umma da 'yan jarida da kasashen duniya su sani cewa gwamnati za su tuhuma idan wani rikici ya barke yayin bikin Ashura a ranar Talata.'

Bayan batakashin da ya faru tsakanin 'yan kungiyar da 'yan sanda a ranar 22 ga watan Yuli da ya yi sanadiyar mutuwar dan sanda, DCP Umar Usman da dan yi wa kasa hidima, Precious Owolabi da 'yan kungiyar IMN 11, gwamnatin tarayya ta haramta ayyukan kungiyar.

A bangarenta, Rundunar 'Yan sandan Najeriya ta gargadi kungiyar kan yin tattakin na Ashura. Kakakin 'yan sanda, DCP Frank Mba ya tabbatar da cewa sufeta janar na 'yan sanda ya bawa kwamishinonin 'yan sanda umurnin dakatar da tattakin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel