Anyi barazanar kashe Mansurah Isah matukar bata tura zunzurutun kudi har dalar Amurka dubu daya da dari biyar ba

Anyi barazanar kashe Mansurah Isah matukar bata tura zunzurutun kudi har dalar Amurka dubu daya da dari biyar ba

Wasu da ake zargin 'yan damfara ne sun aikawa da tsohuwar jaruma kuma sabuwar furodusa a Kannywood matar Sani Musa Danja, wato Mansurah Isah da sakon cewa an umarce su da su kashe ta amma suna so su sasanta da ita

A cikin irin sakonnin da miyagun mutanen suka aika mata sun tabbatar mata da cewa su 'yan Boko Haram ne, kwangilar kashe ta aka ba su kuma a yanzu haka sun kammala dukkan shirin su na aika ta kiyama suna da hotunan ta sunan ta, 'yan'uwanta da abokai da adireshinta da wuraren dabdalar ta, kuma za su iya harbin ta a ko'ina amma sun bata zabin ta tura musu da dalar Amurka dubu daya da dari biyar sai su fasa kwangilar kashe ta din.

Sai dai barazanar ta su ko daya bata bawa Mansura Isah tsoro ba, inda ta mayar musu da martani cikin jarumta ta aika musu da cewa ita bata tsoron mutuwa kana ta wallafa hotunan sakonnin da suka tura mata a shafinta na Instagram gami da rubuta cewa:

"A yayin da nake gwagwarmaya da wannan dan damfarar na tsawon lokaci, yanzu yayi mini barazanar cewar an bashi umarnin ya kashe ni, amma kuma ya ce idan na tura masa dalar Amurka dubu daya da dari biyar zai kyaleni. Ko da yake banga laifinsa ba, idan na ceci rayuwata a wajensa yanzu, wanene zai ceceni daga Allah idan yazo daukar rayuwata?

"Abinda ba su sani ba shine, akwai mutanen da basa tsoron mutuwa. Wallahi da ina da tsoro ko ina tsoron mutuwa ba zan dinga yin aikin taimakon da nake yi ba. Kauyukan da nake shiga wallahi da duka ba zan shige su ba.

"Naje kauyen da sun shafe shekara 50 bako bai shigo musu ba, na shiga na fito lafiya da ikon Allah. Na hau dutse, na tsallaka ruwa, na bi kwale-kwale, naje a mota, na hau doki. Mai ya rage min kuma yanzu.

KU KARANTA: Lakcaran da aka kora a ABU akan lalata da dalibai ya samu sabon aiki a jami'ar KASU dake Kaduna

"Shashasha kawai, wallahi ban so na bashi amsa ba amma ya biyo ni ta WhatsApp bayan naki kula shi a Email dina.

Ta cigaba da cewa: "Oga bari na fada maka, idan ka kashe ni a wannan lokacin wallahi zanyi farin ciki, dama can ina ta tunanin zunuban dana aikata a baya ne, kaga idan ka kashe ni komai yazo cikin sauki kenan.

Idan ina da wannan kudin kana tunanin zaka ganni a Instagram yanzu, zan fita na more kudina ne ni da 'yan uwa da abokanan arziki aradu."

Daga karshe dai ta tabbata 'yan damfara ne da wannan aiki domin kuwa jarumi Baballe Hayatu ma a sashen tsokaci ya tabbatar da cewa shi ma ya taba karo da irin 'yan damfarar na, kuma shima irin amsar da ya basu kenan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel