An bawa yarinya mai shekaru 10 'yar Najeriya aikin koyarwa a kasar Ingila

An bawa yarinya mai shekaru 10 'yar Najeriya aikin koyarwa a kasar Ingila

- Yarinya karama mai suna Emmanuella Mayaki, ta samu aikin koyarwa a wata makarantar firamare dake Coventry a kasar Ingila.

- An bawa Emmanuella aikin koyarwar ne bayan an gano cewa tana da ilimi sosai a bangaren na'ura mai kwakwalwa

- Yariyar ta shawarci gwamnatin Najeriya da ta kawo kayayyakin cigaba da zasu bawa yara damar koyar kwamfuta tun suna kanana

Emmanuella Mayaki yarinya mai shekaru 10 a duniya, ta samu aikin koyarwa bayan ta nuna bajintar ta da kwazo wajen wani aiki da aka yi na na'ura mai kwakwalwa.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa yarinyar tana da kwazo matuka a bangaren manhajar Microsoft kuma har ma ta bude shafi nata a yanar gizo-gizo.

Bayan makarantar firamaren ta Southfields ta gano irin kwakwalwar da yarinyar take da ita da kuma irin kokarin da take nunawa wajen aiki, sai suka bata damar yin aikin koyarwa da su domin ta dinga nunawa yara irinta irin abubuwan da take yi.

KU KARANTA: Abinda yasa shugaba Buhari baya daukar mataki akan masu zagin shi a shafukan sadarwa - Gwamnatin tarayya

Da take magana da jaridar Vanguard, karamar yarinyar ta ce tana so gwamnatin Najeriya ta kawo kayayyaki na cigaba wanda za su saka yara 'yan Najeriya su koyi amfani da na'ura mai kwakwalwa.

Sannan ta kara da cewa a hirar ta su da cewa tana so ta dinga koyawa yara ne saboda ta san cewa fasaha ita ce abar da ake alfahari da ita a duniya yanzu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel