Matsalolin yau da gobe sun tasa wata ‘Daliba har ta kusa hallaka kanta
An samu wata ‘Daliba da ta yi yunkurin daukar rayuwar ta da kan ta a Garin Nsukka da ke jihar Enugu a cikin Kudu maso Gabashin Najeriya. Wannan ya faru ne a karshen makon da ya wuce.
A Ranar Asabar, 8 ga Watan Satumba, 2019, wata Baiwar Allah ta sha maganin kwarin nan da ake kira ‘Sniper’ domin ta kashe kan ta ta huta. Jaridar nan ta Punch ce ta rahoto wannan labari jiya.
Chinwendu Odoh wanda ta karatu a jami’ar nan ta Nsukka, ta nemi ta kashe kan ta ne amma hakan bai yiwu ba bayan an sheka da ita asibiti inda Ubangiji ya tsaga ta na da sauran kwana.
Jami’in da ke magana da yawun ‘yan sanda a Enugu, Ebere Amaraizu, ya tabbatarwa Manema labarai aukuwar wannan abu. Kakakin yace wannan mugun abin ya faru ne Ranar Asabar.
Jawabin ‘yan sanda na cewa: “Wannan Budurwa mai suna Chinwendu Odoh mai shekara 24 a Duniya, ta fito ne daga Garin Enugu Ezike a cikin karamar hukumar Igboeze ta Arewa a jihar.
KU KARANTA:
“Kuma wannan Yarinya, ta na aji biyu a jami’ar Najeriya, UNN ta Nsukka inda ta ke karantar ilmin kananan halittu. Ana zargin ta sha maganin kwarn nan ne na ‘Sniper’ domin ta kashe kan ta.”
An ruga da ita zuwa asibitin Royal Cross da ke cikin Garin Nsukka inda aka dace aka tashi kafadunta. Jami’in ya kuma tabbatar da cewa za a binciki dalilin da ya sa Odoh ta yi wannan aiki.
Sai dai kafin a kammala bincike, an fara gano cewa matsaloli da takaicin gida ne ya jawo wannan Budurwa ta nemi ta kawo karshen rayuwarta. Gidaje da dama su na fama da matsaloli da sabani.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng