EFCC ta fidda sunayen barayin man fetur 58 da ta cafke a Ribas
Hukumar hana yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati a Najeriya EFCC, a reshen ta na birnin Fatakawal da ke jihar Ribas, ta tsunduma cikin binciken wasu mutane 58 da aka zargi da satar man fetur.
Jaridar PM News ta ruwaito cewa, hukumar dakarun sojin ruwa ta Najeriya ce ta cafke ababen zargin tare da jiragensu na ruwa a wani simame da ta kai kuma ta danka su a hannun hukumar yaki da rashawa ta kasar.
Ababen zargin kamar yadda hukumar EFCC ta wallafa sunayen su sun hadar da wani dan kasar Mexico; Daniel Faviel Flore da Khrstoliubov Victor dan kasar Ukraine, sai kuma 'yan Najeriya 56 da suka hadar da Umoh Emmanuel Etim; Aliu Dominic; Okwong Effiong Ukpong; Talick Uche Epuk; Okon Emmanuel Sunday; Ebenezer Marshal; Awuletey Okon; George Obomate; Johnbull Uroro; Alphonomsus Augustine Ufot; Jerome Adele-ekun; Mathew Jacob; Okoye Kachi Fred; Johnwill Austin Omubo; Utibe Peter George; Dickson Amadi; Uzi Chibueze Benard; Israel Essien; Job Wilfred; Emmanuel Joseph Ohwimu; Chinedu Nwachukwu Opara; Pascal Chinedu Nnaji; Okechukwu Chukwueke; Peter Ogar; Olatunji Julius Adedokun; Alabede Maruf Olakunle da Origbo Tekevwe Godwill.
Sauran sun hadar da: Evakpo David; Mbachu Kelvin Okechukwu; Nebeire Onyekachi Philip; Akanbi Oluwaseun Moses; Wonodi Chisom Wisdom; Prince Austine Anyor; Anjorin Rasheed Babatunde da Iffi Francis Chuka.
KARANTA KUMA: Dattijo dan shekara 137 ya mutu bayan sauke duk wani bashi a jihar Zamfara
Sauran ababen zargin sun hadar da; Tom Wisdom Udo; Fasina Isaac Kehinde; Edo Nsongurua; Cookey Fubara; Ayoka Joseph; Benson Nwaya; Akinfenwa Mike; Ahmed A Shehu; Okojie Favour Osahon: John Flash; Edward Modunwa; Eyione Alex; Onyeneke Wisdom Udoka; Nwokeke Wisdom Udoka; Nwokeke Michael S.U; Anyasi Joshua Ikechukwu; Edward Atorkemo Harrison; Ekpeno Benjamin; Rafi Nura Sani, Thompson Deezua da Edwin Ekpoto Omaretshogunwa.
Rahotanni sun bayyana cewa, hukumar sojin ta samu nasarar cafke ababen zargin a jiragen ruwa kuma a lokuta gami da wurare mabambanta cikin birnin Fatakwal na jihar Ribas da laifuka na satar man fetur.
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng