Mulkin kama karya a siyasar Kano ya sanya na fice daga masana'antar Kannywood - Naburiska

Mulkin kama karya a siyasar Kano ya sanya na fice daga masana'antar Kannywood - Naburiska

A yayin wata hira da manema labarai na jaridar Daily Trust, fitaccen jarumin nan wanda ya shahara da barkwanci a masan'antar shirya fina-finan Hausa wato Kannywood, Mustapha Naburiska, ya bayar tabbacin ficewarsa daga masana'antar a yayin da ya zayyana dalilai na karin haske dangane da wannan hukuncin da ya zartar.

Duk da cewar zai ci gaba da shirya fina-finai tare da fitowa a wasannin kwaikwayo da aka shirya a wajen jihar Kano, Naburiska ya shelanta cewa ba zai sake fitowa a wani shirin fim ba na jihar har sai wa'adin gwamnati mai ci a jihar ya kare ko kuma hukuncin da kotun daukaka karar zaben gwamnan jihar ta zartar.

A yayin da bai gushe ba wajen ci gaba da godiya da yi wa kungiyar MOPPAN da AREWA fatan alheri sanadiyar kare martabarsu da kuma dandalin Kannywood, fitaccen jarumin ya ce ba zai iya ba da mulkin kama karya na hukumar tace-tace fina-finan Kano, wadda a cewarsa ta na tafiyar da al'amuranta babu kan gado.

Ya ce kazantar siyasa ta dabaibaye hukumar tace fina-finan Kano inda take cin zarafin 'yan adawa. Ya buga misali da yadda hukumar ta ba da umarnin cafke wasu jaruman masana'antar Kannywood saboda akidarsu ta siyasa da ta sha bam-ban da ta gwamnati mai ci a Kano.

KARANTA KUMA: Ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya 72 sun mutu a bana - Guterres

Ya buga misalai da yadda hukumar ta ba da umarnin cafke mai shirya fina-finai, Sani Rambo, mawaki Sadiq Zazzabi da kuma kamun da aka yi wa Sanusi Oscar a kwana-kwanan duk saboda kasancewarsu magoya bayan jam'iyyar adawa ta PDP.

A karshe, jarumi Naburiska ya kwantar da hankalin masoyansa, inda ya ce zai ci gaba bayyana a wasu fina-finan da aka shirya a wajen jihar Kano kuma za su iya nema tare da kallon su a shafin You Tube da sauran shafuka na yanar gizo.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel