Matasa sun yiwa wani malamin addini dukan tsiya, bayan sun kama shi yana kashe mutane yana tsafi da jininsu

Matasa sun yiwa wani malamin addini dukan tsiya, bayan sun kama shi yana kashe mutane yana tsafi da jininsu

- Matasa sun kama wani babban Fasto a jihar Cross River da yake kashe mutane yana tsafi da su don ya samu kudi

- Matasan sun kone cocin shi kurmus, sun kuma sanyawa gidan shi wuta, kafin nan suka kamo shi suka yi masa dukan kawo wuka

- Matasan sun bayyana cewa Faston yayi amfani da yara kanana guda uku a cikin wannan satin ya kashe su yayi tsafi da jinin su

Mutanen garin Ukelle dake karamar hukumar Yala a cikin jihar Cross River, sun huce haushin su akan wani babban Fasto, bayan sun zarge shi da amfani da mutanen garin wajen yin tsaface-tsafacen shi na neman kudi.

A cewar wani mai amfani da shafin Facebook, James Nicolas, ya ce Faston yayi amfani da yara kanana guda uku makon da ya gabata wajen yin tsafin shi.

Cikin bacin rai matasan garin suka dunguma zuwa cocin shi suka sanya mata wuta, sannan suka wuce gidan shi nan ma suka kone shi kurmus, bayan nan suka kamo shi suka fara jibgar shi.

KU KARANTA: An kama wani malamin firamare a jihar Adamawa da ya bai wa dalibar shi maganin bacci yayi mata fyade har ciki ya shiga

"Wannan shine Faston karyar da yake amfani da mutanen mu wajen yin tsaface-tsafacen shi. Idan ba a manta ba farkon shekarar nan mun kawo rahoton cewa mun rasa kusan mutane biyar, kuma satin da ya gabata wannan munafukin ya kashe mana yara uku a wajen tsafin shi," in ji James.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel