Gwamnan jihar Bauchi ya rantsar da sabbin kwamishinoni

Gwamnan jihar Bauchi ya rantsar da sabbin kwamishinoni

- A ranar juma'a ne Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya rantsar da sabbin kwamishinoni 20 a jihar

- Ya hori sabbin 'yan majalisar zartarwar jihar da su dage wajen dawo da martabar jihar

- Gwamnan ya kara da kiran sabbin kwamishinonin da su zama bayin mutanensu ba bayin iyayen gidansu ba

A ranar Juma'a ne Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya rantsar da sabbin zababbun kwamishinoni 20 a jihar.

A yayin rantsar da sabbin kwamishinonin zuwa majalisar zartarwa ta jihar, gwamnan ya dora mu su alhakin wanko ma'aikatan bogi da ke karbar albashi a jihar.

Ya umarce su da su fito da tsarin aiyuka a duk ma'aikatunsu.

Ya hori kwamishinonin da su taka rawar gani wajen tabbatar da sabbin tsare-tsare a jihar.

KU KARANTA: Gwamnan jihar Zamfara ya amince da dawo da malaman makaranta 556 da gwamnatin Yari ta kora

"Aiyukan ku a matsayin 'yan majalisar zartarwar jihar shine ku taka rawa wajen tabbatar da sabbin dokokin jihar da kuma aiwatar dasu."

"A yayin aiwatar da aiyukan ku, za a tunatar da ku cewa duk kwamishinoni daya suke kuma alhakin daukar nauyin duk hukuncin da aka yake a majalisar ya rataya akanku domin hakkinku ne," inji shi.

Mohammed ya ce ya yanke hukuncin samar da gwamnati mai nagarta ne ta hanyar zaben mutane nagari masu dattako a matsayin kwamishinoni.

"Burinmu na samu gwamnati ingantacciya da za ta dawo da martabar mutanenmu ba zai cika ba matukar ba mu samu nagartattun mutane ba a majalisar zartarwar jihar."

"Wadanda muka zaba, mutane ne masu ilimi kuma sun san matsaloli da kalubalen da jihar ke fuskanta. Mutane ne da aka gwada kuma an yarda dasu," ya kara da.

Gwamnan ya kara da horon sabbin kwamishinonin da su zama bayin mutane ba bayin iyayen gidansa ba, su kuma tuna da rantsuwar da suka yi ga ubangijinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel