Bayan Mugabe, kasar Zimbabwe ta sake rashi na wani babban jigonta

Bayan Mugabe, kasar Zimbabwe ta sake rashi na wani babban jigonta

Tsohon shugaban hafsan sojin kasar Zimbabwe, Manjo Janar Trust Mugoba ya mutu. A bisa wani jawabi da shafin ZimLive ta wallafa a Twitter, kakakin gwamnatin kasar, Nick Mangwana ya tabbatar da mutuwar Janar Mugoba.

Mogoba ya mutu ne a wani asibitin kudi a Harare mako guda bayan kwantar dashi.

Nick Mangwana ya sanar cewa tsohon shugaban sojin ya mutu sakamakon wani rashin lafiya da ba a bayyana ba.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Mogoba dai ya mutu ne rana guda da tsohon shugaban kasar na Zimbabwe, Robert Mugabe.

A baya legit.ng ta rahoto cewa Robert Mugabe tsohon Shugaban kasan Zimbabwe ya rigamu gidan gaskiya inda ya rasu ya na da shekaru 95 a duniya. Shugaba Emmerson Mnangagwa ne ya fitar da wannan sanarwa.

KU KARANTA KUMA: Sunayen shuwagabannin kasashen Afirka 15 da aka musu juyin mulki daga 201 zuwa 2019

Shugaba Mnangagwa ya bayar da sanarwar rasuwar ne a ranar Juma’a inda ya bayyana tsohon Shugaban kasan a matsayin jigo wanda ya sha gwagwarmaya domin ganin cigaban kasarsa.

“Gaba daya rayuwarsa ta kare ne a kan nemawa kasarsa da ma nahiyar Afirka gaba daya ‘yanci, tabbas nahiyar Afirka ba za ta taba mantawa da shi ba, Allah ya sa ya huta.” Inji Mnangagwa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel