Inda zuwa yawon bude ido ne kaine a kan gaba, amma yanzu da yake mutane ake kashewa shine ka tura wasu suje - Dino ya caccaki Buhari

Inda zuwa yawon bude ido ne kaine a kan gaba, amma yanzu da yake mutane ake kashewa shine ka tura wasu suje - Dino ya caccaki Buhari

- Sanatan jihar Kogi ta yamma, Sanata Dino Melaye ya mayarwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari martani

- Ya mayarwa da shugaban kasar martani ne akan maganar da yayi game da kisan 'yan Najeriya a kasar Afrika ta Kudu

- Sanatan ya bukaci shugaban kasar da ya jagoranci tawagar da za ta je kasar Afrika ta Kudu din, tunda shima ya taba rike mukamin Janar

Sanata Dino Melaye ya mayarwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari martani akan rubutun da ya wallafa a Twitter akan harin da ake kai wa 'yan Najeriya a kasar Afrika ta Kudu. Ya shawarci shugaban kasar ya jagoranci zuwa kasar koda sau daya ne.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya wallafa wani rubutu a shafinsa na Twitter dangane da harin da aka kai kan 'yan Najeriya a jiya Talata. Sai dai kuma wasu 'yan Najeriya da Sanatoci, sun nuna rashin jin dadin su, cikinsu kuwa harda Sanata Dino Melaye.

KU KARANTA: An sanya mana tsanar junanmu tun lokacin da aka halicce mu - Cewar wasu mutane akan kisan da ake yiwa 'yan Najeriya a Afrika ta Kudu

Shugaba Buhari ya ce: "Zan tura tawaga ta musamman ga shugaban kasar Afrika ta Kudu Ramaphosa domin nuna rashin jin dadin mu akan matsalar rashin tsaro da mutanen mu 'yan Najeriya suke ciki, kuma muna so mu tabbatar da cewa kasar Afrika ta Kudu tana yin iya bakin kokarinta wajen kawo karshen wannan lamarin," in ji Buhari.

A martanin da ya mayar, Dino Melaye ya ce, "Inda ace zuwa yawon bude ido ne ko kuma zuwa duba lafiya, kai ne mutum na farko da zai fara zuwa. Lokaci yayi da ya kamata ka fara fita kana magana akan abubuwan da suke damun mutanen ka, shine zaka tura wasu suje, ba ka taba rike mukamin Janar bane? Kamata yayi ka jagoranci tawagar koda sau daya ne."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel