Buhari ya gana da kungiyar Injiniyoyi ta Najeriya

Buhari ya gana da kungiyar Injiniyoyi ta Najeriya

Mun samu rahoton cewa a halin yanzu shugaban kasa Muhammadu Buhari na tsaka da ganawa da mambobin kungiyar injiniyoyin Najeriya NSE a cikin fadarsa ta Villa da ke babban birnin kasar nan ta tarayya.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, wannan ganawa ta fara gudana ne cikin babban ofishin shugaban kasa da ke fadar Villa da misalin karfe 11.30 na safiyar yau ta Laraba, 4 ga watan Satumban 2019.

Ana iya tuna cewa, shugaban kungiyar Injiniyoyin Najeriya, Engr. Adekunle Mokuolu, ya kasance cikin tawagar gwamnatin tarayya da ta halarci taron bunkasa nahiyyar Afirka karo na bakwai da aka gudanar a shekarar da muke ciki a birnin Tokyo na kasar Japan.

Shugaban kasa Buhari da shugabannin kasashen Afirka, sun ziyarci birnin Tokyo na kasar Japan domin halartar babban taron bunkasa nahiyar Afirka, wanda aka gudanar a tsakanin ranar 28 zuwa 30 ga watan Agustan da ya gabata.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, gwamnatin Japan ce ta jagoranci wannan taro karo na bakwai tare da hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya, Bankin Duniya da kuma kungiyar Tarayyar Afrika AU.

KARANTA KUMA: EFCC ta kama madamfaran yanar gizo 60 a Akwa Ibom

Babu shakka taro ne na kasa da kasa wanda ake mayar da hankali kan bunkasa nahiyar Afirka, wanda kasar Japan ta kaddamar a shekarar 1993.

A baya dai ana gudanar da taron duk bayan shekaru biyar har zuwa shekarar 2016 inda aka fara gudanar da shi bayan shekaru uku, lokacin ne aka gudanar da shi a birnin Nairobi na kasar Kenya.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel