Ana bin kamfanin KEDCO bashin kudi Naira Biliyan 23 na wuta inji TCN

Ana bin kamfanin KEDCO bashin kudi Naira Biliyan 23 na wuta inji TCN

Kamfanin TCN mai alhakin bada wuta a Najeriya ya hakikance a kan cewa ana bin kamfanin KEDCO masu raba wuta a jihar Kano da kewaye, bashin kudi na sama da Naira biliyan 20.

TCN na cewa a cikin watan Mayun 2019, akwai bashin Naira biliyan 23 a kan kamfanin KEDCO. Kamfanin TCN sun ce masu wuta su na bin KEDCO wannan kudi da ta ke ta faman musanyawa.

Haka zalika TCN ta ce babu wani bashin da DisCos ke bin ta kamar yadda ake ikirarin cewa akwai wasu kudi da ba ta gama biya ba. TCN sun bayyana wannan ne ta wani jawabi da su ka fitar a jiya.

Kamfanin na TCN na Najeriya ta ce ta dakatar da KEDCO ne tare da sauran kamfanonin da ke raba wuta a yanin Ribas - Fatakwal, Legas - Ikeja, Enugu a dalilin wani tarin bashin da ake binsu.

KU KARANTA: An fasa yin taron Ministocin wannan makon a Najeriya

Jawabin na TCN ya nuna cewa duk sauran kamfanoni sun biya bashin da ake bin su face KEDCO. Kamfanin KEDCO na zargin TCN da rike mata wasu kudinta don haka har ta rika saba doka.

Rahotannin da mu ke samu sun nuna KEDCO ta na ikirarin cewa kudin ta da su ka makale a hannun TCN ne ya sa su ka rika sabawa dokokin kasuwanci da hukumar TEM ta gindaya a kasar.

TCN ta nuna cewa sam babu ruwanta inda ta ce babu wani bashi da KEDCO ke bin ta a daidai watan Mayun 2019. TCN tace sai dai ma KEDCO ne ake bi bashin kudi a kaf shekarar 2015.

Kamfanin da ke bada wuta a kasar ta zargi KEDCO da karbar kudin lantarki a shekarar 2015 ba tare da cirewa ‘yan kasuwa kasonsu ba duk da kuwa da sunansu ake karbar kudin daga jama’a.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel