Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da mahaifiyar hadimin gwamna Badaru

Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da mahaifiyar hadimin gwamna Badaru

Wasu gungun yan bindiga da suka yi awon gaba da mahaifiyar Alhaji Yahaya Muhammad, tsohon mashawarcin gwamnan jahar Jigawa, Badaru Abubakar a kan har siyasa, sun nemi kudin fansa na naira miliyan 50 kafin su saketa.

Jaridar Dialy Trust ta ruwaito yan bindiga sun yi garkuwa da tsohuwar mai suna Hajiya Ladi ne da sanyin safiyar ranar Talata, 3 ga watan Satumba a gidanta dake kauyan Kaya, cikin karamar hukumar Suletankarkar na jahar Jigawa.

KU KARANTA: EFCC ta baza komarta tana farautar wani dan takarar shugaban kasa a Najeriya

Wani daga cikin dangin matar ya bayyana cewa an fara tattaunawa da yan bindigan game da kudin da suka nema kafin su saketa, sun bukaci a biyasu naira miliyan 50, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito shi.

Da aka tuntubi rundunar Yansandan jahar Jigawa game da lamarin kuwa, sai kwamishinan Yansandan jahar, Bala Zama Sanchi ya tabbatar da aukuwar lamarin, sa’annan ya bada tabbacin Yansanda za su cigaba da bin diddigin lamarin don ceto tsohuwar.

A wani labari kuma, wasu gungun yan bindiga masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da wani kusa a jam’iyyar PDP, kuma shugaban matasan jam’iyyar, Sunday Udeh-Okoye a ranar Litinin, 2 ga watan Satumba a gonarsa dake kauyen Ohumagu, a yankin Agbaogwugwu na jahar Enugu.

Kaakakin rundunar Yansandan jahar Enugu, Ebere Amaraizu ya tabbatar da sace shugaban matasan na PDP, inda yace suna bin diddigin lamarin tare da bin sawun yan bindigan. Sai dai har yanzu babu tabbacin ko yan bindigan sun tuntubi iyalan Mista Sunday.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel