Davido ya shirya tsaf don angwancewa da amaryarsa

Davido ya shirya tsaf don angwancewa da amaryarsa

- Shahararren mawaki Davido, ya shirya tsaf don auran rabin ransa Chioma

- Mawakin ya bayyana hakan ne a shafinsa na twitter Inda ya baza hotunan gaisuwa da ya kai ga danginta

- Ya sanar da abokai da masoya da su shirya don gagarumin bikin a shekarar 2020

Shararren mawaki Davido, ya shirya tsaf don auren rabin ransa Chioma. Mawakin dai har ya kai gaisuwa ga dangin masoyiyar ta sa.

Angon mai jira gado ya Samar da hakan ne a shafinsa tare da sanar da cewa za a yi shagalin aurensu a 2020.

Ya qara da baza hotunansa da masoyiyar tasa na gaisuwar da ya kai ga danginta. Ya sanar da abokai da masoya da su shiryawa gagarumin bikin.

DUBA WANNAN: Aiki na shine kashe kudade a matsayina na gwamna - Abdulaziz Yari

Kamfanin Dillancin Labarai ya ruwaito cewa Shahararren mawaki Davido ya zuba hotunansa da na masoyiyarsa a shafinsa na twitter da taken "Abu na farko dai, gaisuwa".

Masoya suna ta dai san barka tare da taya shahararren mawakin murnar sabuwar cigaban.

Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ya ruwaito cewa mawakin dai ya bayyana niyyarsa na auren Chef Chioma Rowland ne a wani lokaci na tambaya da amsa da ya ba masoyansa a shafinsa na twitter.

Davido ya yi amfani da damar wajen kore jita-jitar da ke bayyana rabuwarsa da masoyiyar ta sa.

"Chioma ta goge shafinta na Instagram ne don ta mayar hankali kan girke-girkenta." Inji mawakin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel