Kotu ta kashe auren shekaru 8 saboda duka

Kotu ta kashe auren shekaru 8 saboda duka

- Wata kotun shari'a da ke Kaduna ta kashe auren shekaru 8 a kan duka

- Rashida Yakubu wacce ta kai karar mijinta ta ce bayan matsalar da suke samu akwai duka da rashin kula

- Mai shari'ar ya bukaci magabatan ma'auratan da su sasantasu amma abin yaci tura

A yau Talata ne wata kotu dake Kaduna ta kashe auren shekaru 8 tsakanin Rashida Yakubu da mijinta, Muhammad Yahaya, akan batiri.

Mai shari'ar, Murtala Nasir, ya kashe auren ne bayan kokarin da yayi kan magabatan ma'auratan su sasantasu.

"Tunda Yahaya ya kasa gabatar da shaidunsa don karyata abinda matarsa ta sanar, kotu zata yanke hukunci ne bisa ga abinda magabatan ma'auratan suka yarda," inji alkalin.

DUBA WANNAN: Kwace kadarorina tauye hakkina ne da kundin tsarin mulki ta bani - Diezani

Tun farko dai dama mai karar, Rashida Yakubu ta roki kotu da ta karbar mata saki wajen maigidan nata, saboda batiri da kuma rashin kula.

"Mijina dama ya saba dukana. Ya taba korata kuma ya sayar da kaya na," cewarta.

A kokarin kare kansa, Yahaya ya musanta abinda matarsa ta sanarwa da mai shari'a.

Ya sanar da kotun cewa shi fa yana kaunar matarsa kuma ya bukaci alkalin da ya bashi lokaci don rokar gafararta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel