Wani Mahaifi ya kashe dan sa da ya saci N500 a Akwa Ibom

Wani Mahaifi ya kashe dan sa da ya saci N500 a Akwa Ibom

Hukumar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Akwa Ibom, ta cafke wani matashin mahaifi mai shekaru 35 a duniya, Idorenyin Essien, bayan ya kone dan sa kurmus har lahira da ya saci N500 a karamar hukumar Eket ta jihar.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, kakakin hukumar 'yan sandan jihar, Odiko Mac-Don Achibe, ya bayar da tabbacin wannan mummunan lamari da cewar ya auku ne a ranar juma'ar da ta gabata cikin yankin Afis Nsit na karamar hukumar Eket.

Achibe wanda bai furta sunan mamacin ba, ya dai bayyana cewa jami'an 'yan sanda da ke sintiri a unguwar Eket, sun damke mahaifin sa a cikin gidan da ya aikata wannan ta'asa.

Kakakin 'yan sandan ya ce za a gurfanar da Mr Essien a gaban kuliya da zarar bincike ya kammala, inda zai fuskanci fushin doka kwatankwacin laifin da ya aikata.

Wani jagoran al'umma a yankin Afia Nsit ya ce, Essien ya kone dan sa kurmus har lahira bayan da wani makocin sa mai sayar da kayan abinci ya zarge shi da satar naira dari biyar.

Okon ya ce "mahaifin bayan biyan makocin sa wannan kudi, ya kuma yi wa dan nasa fada da kyara irin ta iyaye."

Da ga bisani kuma, "Mahaifin ya aiki dan sa cikin gaggawa inda ya nemi ya sayo masa makamashin kalanzir ba tare da ya san abin da mahaifin nasa ya kudirta a zuciyar sa ba."

KARANTA KUMA: Xenophobia: 'Yan Najeriya za su kauracewa sayan kayayyakin kasar Afirka ta Kudu

"Dawowar dan na sa ke da wuya, Mr Essien ya yi masa daurin dabaibayi hannu da kafa da igiya, inda ya antaya masa kalanzirin tare da cinna masa wuta kuma ya koma gefe guda yana kallon dan sa na ci da wuta a harabar gidan sa."

An yi gaggawar garzayawa da dan sa zuwa asibitin kurkusa in da a nan ya ce ga garin ku nan, lamarin da ya sanya makota suka ankarar da hukumar 'yan sanda kuma a cafke mahaifin ba tare da wata-wata ba.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel