Innalillahi: Yadda Malam Musa ya kama amaryarsa Fatima tana zina da dan cikinsa akan gadonsu na Sunnah

Innalillahi: Yadda Malam Musa ya kama amaryarsa Fatima tana zina da dan cikinsa akan gadonsu na Sunnah

- Wani mutumi ya kama matarsa mai suna Fatima tana zina da dan cikinsa

- Mutumin mai suna Musa Akur dan shekara 49 ya kama matar ta sa da dansa Audu a yayin da ya kai ziyara gidan dan nasa bayan ya dawo daga wajen kasuwanci

- An bayyana cewa bayan kama su din da yayi ashe dama Audu har ya riga ya yiwa matar mahaifin nasa ciki

Wani abu mai rikitarwa da ban mamaki da ya faru a kauyen Honko, dake karamar hukumar Awe cikin jihar Nasarawa, ya nuna yadda wata mata ta samu ciki da dan kishiyarta.

Haka kuma mijin matar ya sake kama ta dumu-dumu tana yin lalata da dan nasa na cikinsa. Wannan labari dai ya faru akan mutane uku ne, Fatima Musa mai shekaru 33 wacce ta auri mahaifin Audu mai suna Musa Akur mai shekaru 49.

Mahaifiyar Audu dai ta rasu shekaru tara da suka wuce, hakan ya sanya mahaifinsa wanda yake manomi ne ya nemo wata domin ya kara aura. Bayan ya auro ta biyun kuma sai ya sake yanke shawarar auro wata ta uku.

Wannan dalilin ne yasa rikici ya barke a gidan, duk lokacin da magana ta tashi Musa yana shan zagi a wajen Fatima akan irin yadda yake nuna rashin adalci tsakaninta da sabuwar matar da ya auro mai suna Hausa.

Haka kuma Fatima ta bayyana cewa baya bata hakkinta na kwanciyar aure, inda ta bayyana cewa yanzu kusan shekara daya kenan rabon da ya kwanta da ita.

KU KARANTA: Sama da wata daya kenan: Har yanzu ba a san inda aka gudu da mai sukar gwamna Ganduje ba

A watan Janairun wannan shekarar ta 2019, Fatima wacce take samun halin ko in kula daga wajen mijinta an same ta rungume da Audu, wanda yake shine da daya tilo ga mahaifiyarsa da ta rasu. Fatima ta fara soyayya da shi bayan ta gaji da zama babu kulawar miji.

Yawan zuwa dakin Audu da take yi yasa mutane suka fara zarginta, hakan yasa jita-jita ta fara yaduwa cewa akwai wani abu dake tsakanin Fatima da Audu.

Haka kuma Musa ya taba yi musu gargadi akan irin matsalar dake tattare da irin wannan dangantakar ta su, inda ya nemi Fatima da ta daina zuwa dakin Audu, sai dai Fatima ta nuna cewa babu abinda ke tsakaninta da shi.

Ana haka kawai sai ganin ciki aka yi ya fito a jikin Fatima, sannan kuma bayan wata uku da samun cikin Malam Musa ya sake kama su dumu-dumu suna lalata akan gado. Wannan lamari ya sa jama'a suka yi caa akan su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel