Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da wani babban jigo a jam’iyyar PDP

Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da wani babban jigo a jam’iyyar PDP

Wasu gungun yan bindiga masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da wani kusa a jam’iyyar PDP, kuma shugaban matasan jam’iyyar, Sunday Udeh-Okoye, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan bindigan sun yi awon gaba da Sunday ne a ranar Litinin, 2 ga watan Satumba a gonarsa dake kauyen Ohumagu, a yankin Agbaogwugwu na jahar Enugu.

KU KARANTA: EFCC ta kwato naira N801,307,562 daga barayin gwamnati a jahar Kano Read

Kaakakin rundunar Yansandan jahar Enugu, Ebere Amaraizu ya tabbatar da sace shugaban matasan na PDP, inda yace suna bin diddigin lamarin tare da bin sawun yan bindigan. Sai dai har yanzu babu tabbacin ko yan bindigan sun tuntubi iyalan Mista Sunday.

A shekarar 2017 aka zabi Sunday a matsayin shugaban matasan PDP yayin da yake dan majalisar dokokin jahar Enugu, amma daga bisani ya yi murabus da mukamin dan majalisar inda ya koma babban birnin tarayya Abuja.

Matsalar garkuwa da mutane ta zama ruwan dare a Najeriya, sakamakon ta mamaye dukkanin sassan kasar nan, daga Arewa zuwa Kudancin kasar nan, babu inda ya sha game da matsalar satar mutane da garkuwa da su.

A wani labarin, gungun miyagun yan bindiga masu garkuwa da mutane sun kai wani samame zuwa kauyen Yandaka dake cikin karamar hukumar Batsari, ta jahar Katsina inda suka yi ma Maigari Yandaka dukan tsiya tare da harbinsa.

Yan bindigan sun kai wannan hari ne a daren Asabar, 31 ga watan Agusta, inda bayan sun jikkata Maigarin a kai da hannu, sai kuma suka tasa keyar Matarsa da yayansa 3, suka yi awon gaba dasu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel