Garba Shehu: Iyaye ne Talakawa ne, dagewa na yi, har na zama wani

Garba Shehu: Iyaye ne Talakawa ne, dagewa na yi, har na zama wani

Malam Garba Shehu a wata hira da yayi da Onyebuchi Ezigbo kwanan nan, ya bada labarin rayuwarsa inda ya taso a karamin gida har ta kai ya zama babban Hadimin shugaban kasa.

Garba Shehu yace an haife sa ne a cikin Garin Dutsen da ke birnin Jigawa a yanzu. A wancan lokaci, ba kowa bane ya ke samun damar karatun Boko. Shehu yace Mahafinsa Direban mota ne.

Haka zalika babban Hadimin na shugaba Buhari ya ce Mahaifiyarsa sukari ta ke saidawa a lokacin yana karami. Shiyasa har gobe yake son cin kayan zaki da zarar ya ga kayan kwalama.

Hadimin shugaban kasar Najeriyar yace fadi-tashi yayi har ya samu ilmi, yau ga shi ya kai inda ya kai. Shehu yace ga mai neman nasara a rayuwa, babu wata dabara face ya dage, ya tashi tsaye.

A wannan hira, Malam Garba Shehu ya bada labarin yadda Marigayi Mai martaba Ado Bayero ya taba zuwa Makarantarsu a lokacin ya na karami inda ya amsa wata tambaya da Sarkin yayi masu.

KU KARANTA: Minista Pantami ya dauki matakin gyara ma’aikatar sadarwan Najeriya

Tsohon ‘Dan jaridar yace wannan ziyara da Sarkin Kano ya kawo masu har ya rike masa hannu, ya kuma fada masa wasu kalamai, yana cikin abin da ya tunzurasa har ya kai ga nasara a rayuwa.

A game da labarin soyayya kuwa yace ya yi aure ne a lokacin yana da shekaru 27 a Duniya bayan ya dade yana addu’a ya hadu da wanda zai aura, inda yace yana ganinta ya san ya ga matarsa.

Daga cikin lokacin da Shehu ya sha wahala a rayuwa shi ne lokacin da zai rubuta jarrabawar WAEC ta kammala Sakandare. Da farko ya ce ya yi wasa, amma daga baya ya dage, ya samu sa’a.

A doguwar hirar Hadimin shugaban kasar yayi, ya ce lokacin da ya yi farin ciki da yana karami shi ne sa’ilin da aka saya masa kayan sallah, sannan ya ce babu abin da yake tsoro irin mutuwa.

Yau dai ga shi da Malam Garba Shehu ake shiga cikin zauren majalisar dinkin Duniya da fadar shugaban kasar Amurka, da sauran manyan Biranen Duniya tare da shugaban kasar Najeriya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel