Manyan masu laifi 10 da hukumomin tsaro ke nema a Najeriya

Manyan masu laifi 10 da hukumomin tsaro ke nema a Najeriya

A makon da ya gabata ne hukumar tsaro da binciken diddigi ta kasar Amurka FBI, ta cafke wasu 'yan Najeriya 77 da ake zargin su da aikata miyagun laifuka na zambar dukiyoyin al'umma ta hanyar intanet, wato yanar gizo.

Wannan lamari ya sanya hukumar hana yiwa tattalin arziki zagon kasa ta Najeriya EFCC tare da hadin gwiwar hukumar FBI ta Amurka, suka dukufa wajen gudanar da binciken hadin kai domin damko masu hannu cikin wannan muguwar aika-aika ta 'yan damfara da ke kasar nan.

Biyo bayan wannan lamari, yawan 'yan Najeriya wadanda ake zargi kuma hukumomin tsaro na cikin gida da waje ke nema ruwa a jallo ya karu.

Kamar yadda muka kalato daga jaridar The Punch, ga wasu kasurguman masu laifi 10 wadanda suka yi wa hukumomin tsaro layar zana a yayin da ake ci gaba da neman su ruwa a jallo sanadiyar miyagun laifuka da suka aikata.

1. Valentino Iro

Hukumar FBI ta kasar Amurka na ci gaba da neman Valentino mai shekaru 31 tare da abokin huldarsa, Chukwudi Igbokwe mai shekaru 38, a sakamakon damfarar miliyoyin dukiya ta hanyar yanar gizo.

2. Mrs Ngozi Olejeme

Ana ci gaba da neman Ngozi ruwa a jallo a sanadiyar yin ruf da ciki kan dukiyar kasa ta kimanin naira biliyan 69 ta hanyar zambo cikin aminci. Ana zargin tsohuwar shugaban asusun inshora na NSITF, wato Nigeria Social Insurance Trust Fund, ta tsere da dukiyar ma'aikatar ta kimanin naira biliyan 65 tare da wasu manyan abokanan aikin ta, Mista Umar Abubakar da kuma Mrs Theresa Ittu.

Olujeme 'yar asalin karamar hukumar Oshimili ta Kudu ta birnin Asaban jihar Delta, ta tsere bayan kama ta da laifin zambar dukiya da ta aikata har kashi biyu tare da wasu mutane; Prof. Olufunmilade Adeyemi, Haruna Adamu Gazau, Jennifer Turnah, da kuma 'yan kasar Chana biyu; Liang Zhang, Junyuang Jiang, da kuma Christopher Achebe.

3. Government Ekpemupolo

Hukumar EFCC na ci gaba da neman Mista Ekpemupolo ruwa a jallo biyo bayan laifin da ya aikata na zambar kimanin naira biliyan 45.5. Ekpemupolo wanda ya kasance tsohon shugaban tsagerun Neja Delta, mai amfani da inkiyar Tompolo, ya yi layar zana tun a watan Fabrairun 2016 da babbar kotun tarayya ta Legas ta bayar da umarni kama shi da laifin handama da babakere ta kimanin naira biliyan 45.5.

Hukumar EFCC ta na tuhumar Tompolo da kuma wasu mutane 4 cikin wannan mummunar harkalla ta yashe dukiyar gwamnati da suka hadar da; Kime Engozu, Rex Elem, Gregory Mbonu da Capt. Warredi Enisuoh. Haka zalika tuhumar ta hadar da wasu kamfanoni hudu; Global West Vessel Specialist Ltd., Odimiri Electrical Ltd., Boloboere Property da kuma Estate Limited and Destre Consult Ltd.

4. Ittu Theresa

Ya zuwa yanzu hukumar EFCC na ci gaba da neman Theresa ruwa a jallo, bayan ta yi awon gaba da dukiyar gwamnatin Najeriya ta kimanin naira biliyan 1 a wani kwantaragi da ta kulla na yaudara.

Mrs Theresa ta kuma damfari wani kamfanin kasar Rasha dukiya ta kimanin dalar Amurka miliyan 1.4, bayan kulla wata harkallar kasuwanci inda ta karbe sassan jiragen sama kuma ta tsere ba tare da ta biya ba.

5. Aisha Shettima Nur

Aisha Nur, ma'aikaciyar banki wadda ta kasance 'yar asalin jihar Borno mai jin yaren Turanci, Hausa da kuma na Kanuri, ta yi aron kafar kare tun a watan Nuwamba na shekarar 2016 yayin da hukumar EFCC ta bankado wata kutungwilar ta zambar dukiya kashi-kashi har guda goma.

6. Ijeoma Ugwah

Mrs Ugwah mai shekaru 61 'yar asalin karamar hukumar Owerri ta Arewa a jihar Imo, ta danna layar zana bayan da hukumar EFCC ta bankado laifin da ta aikata na damfara dukiya har kashi ta dalara Amurka miliyan 10 da kuma naira miliyan 4

7. Idris Usman

Hukumar EFCC na zargin Alhaji Usman da laifin almundahana ta naira biliyan 1 na asusun SURE-P. Hukumar dai ta na neman sa ruwa a jallo bayan cinye naira biliyan daya kudin wata kwangila da ya karba a hannun tsohon gwamnan jihar Katsina, Alhaji Shehu Shema, wanda ake ci gaba da zarginsa kan almundahana ta dukiyar gwamnati ta kimanin naira biliyan 11.

8. Anthony Onetule

Hukumar 'yan sandan kasa-da-kasa Interpol, na neman Anthony Onetule ruwa a jallo sanadiyar laifin da ya aikata na leken asirin wata komfuta ba tare da izini ba, inda ya tafka gagarumar da sace-sace da ta janyo asarar dukiya mai tarin yawa.

KARANTA KUMA: Kada a ga laifi na kan hukuncin $9bn da gwamnatin Birtaniya ta zartar - Malami

Bakin haure da ake nema ruwa a jallo:

9. Susan Elya

Susan Elya, 'yar asalin kasar Australia, ana zargin ta da laifin zamba ta kimanin naira miliyan 20. Mrs Elya mai shekaru 41 wadda wurin zamanta na karshe kafin ta arce ya kasance gida mai lamba 11 a layin Vernam na unguwar Maitama ta birnin Abuja, ta yi damfarar kudi har kimanin naira miliyan 20.

10. Doron Umansky

Doron Umansky, dan asalin kasar Isra'ila ne wanda ya zama gwani a yaren Yarbanci, Turanci da kuma yaren Yahudawa, ya tsere daga kasar nan bayan ya aikata miyagun laifuka na zambar dukiyar al'umma.

Usmansky mai shekaru 57 a duniya, ya aikata wannan miyagun laifuka tare da wasu abokanan huldarsa biyu wanda suma ake nemansu ruwa a jallo; Hannah Sobowale da kuma Hammed Ariyomi.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel