Yanzu-yanzu: Ali Nuhu ya karyata labarin da ake yadawa na cewa jarumar Indiya ta wulakanta shi

Yanzu-yanzu: Ali Nuhu ya karyata labarin da ake yadawa na cewa jarumar Indiya ta wulakanta shi

- Fitaccen jarumi Ali Nuhu ya karyata labarin da ake yadawa akan shi na cewa jarumar Indiya ta yi masa wulakanci

- Jarumin ya bayyana cewa wannan labari bashi da tushe bare makama, inda kuma ya bukaci masoyansa da suyi watsi da wannan labari na kanzon kurege

- Idan ba a manta ba makonnin da suka gabata labari yayi ta yawo wanda ke nuna cewa jarumar Indiya ta yi burus ta kyale jarumin bayan ya aika mata sakon murnar ranar haihuwarta

Idan ba a manta ba kwanakin baya mun ruwaito wani labari da muka samu daga jaridar Dabo FM wanda ke nuni da cewa fitacciyar jarumar Indiya Shraddha ta wulakanta fitaccen jarumi Sarki Ali Nuhu a yayin da ya tura mata sakon murnar ranar haihuwarta.

Bayan wani kiran waya da muka samu daga wajen fitaccen jarumin ya bayyana mana cewa wannan labari da ake watsawa bashi da tushe bare makama, ma'ana labarin kafafen sadarwar suka yada a wancan lokacin akan shi labari ne na kanzon kurege.

KU KARANTA: Tirkashi: An bayyana wani birni a Najeriya da ya fi kowanne birni hadari a duniya

Ba wannan ne karo na farko da aka fara yada labari na kanzon kurege game da jaruman na Kannywood ba, musamman fitattu irinsu jarumi Sarki Ali Nuhu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng