An kashe mutum 1 yayinda magoya bayan APC suka kara a jihar Niger

An kashe mutum 1 yayinda magoya bayan APC suka kara a jihar Niger

Rahotanni sun kawo cewa wani rikici da ya barke tsakanin yan takarar Shugaban karamar hukuma na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), a zaben karamar hukuma da za a yi a watan Nuwamba a jihar Niger ya yi sanadiyar mutuwar mutum guda sannan wasu da dama sun jikkata.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, lamarin ya afku ne a hanayr Minna zuwa Bida a ranar Alhamis, bayan yan takarar sun yanki fam din takara a zaben Shugaban karamar hukumar Katcha.

Wanda abun ya ritsa dashi da aka ambata da suna Abubakar Nda-Bida ya kasance magoyin bayan Alhaji Danjuma Eindachi, daya daga cikin yan takarar.

Wasu idon shaida sun bayyana cewa magoya bayan dayan dan takarar wanda aka ambata da suna Alhaji Musa Ishyaku da magoya bayan Emindachi sun kara da juna a gadar kogin Gbako inda lamarin ya afku.

An tattaro cewa mambobin kungiyar biyu sun yi amfani da muggan makamai kamar su adda, takobi, da wukake, inda hakan yayi sanadiyar mutuwar Nda-Bida tare da wasu da dama da suka jikkata.

Shugaban jam’iyyar a jihar, Alhaji Jibrin Imam, ya tabbatar da labarin, inda ya bayyana larin a matsayin “ta’addanci”.

KU KARANTA KUMA: TICAD7: Buhari ya baro Japan yana a hanyar zuwa Abuja bayan halartan taro

Kakakin rundunar yan sandan jihar, DSP Muhammad Abubakar, ma ya tabbatar da lamarin, cewa “an kama mutum guda da ke da nasaba da lamarin.”

Ya roki mambobin jam’iyyun siyasa masu rijista da su yi takunsu daidai da doka a lokaci da bayan zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel