Abu dai sai gaba yake yi: Aisha Idris ta sake cin mutuncin Ali Nuhu da yaransa inda ta yi musu tatas

Abu dai sai gaba yake yi: Aisha Idris ta sake cin mutuncin Ali Nuhu da yaransa inda ta yi musu tatas

- Aisha Idris ta sake bayyana a wani sabon bidiyo ta sake ciwa Ali Nuhu da yaransa mutunci

- Ta bayyana cewa baza ka taba jin yaransa sunyi magana ba lokacin da aka yi magana akan addini, amma da an tabo maigidansu sai su bi su ishi kowa

- Ta kara da cewa duk macen da Ali Nuhu ya dauka ya saka a harkar fim ba taimakar ta yayi ba kanshi ya taimaka saboda kudi yake samu da ita

A irin wutar rikicin da ke cigaba da ruruwa a masana'antar fina-finan Hausa ta Kannywood, har yanzu ana cigaba da samun kace-nace a wajen mutane tun bayan lokacin da aka kama darakta Sunusi Oscar 442.

Daya daga cikin wacce ta yi kaurin suna wajen cin mutunci da kuma zagin wadanda ake zargin suna da hannu a kama daraktan ita ce Aisha Idris, wacce a kwanakin baya ta bayyana a wani bidiyo ta zazzagi jarumi Ali Nuhu da shugaban hukumar tace fina-finai na jihar Kano Isma'ila Na'Abba Afakallahu.

KU KARANTA: Hadiza Gabon ta tallafawa Maryam KK da makudan kudade akan iftila'in da ta fada na shiga hannun 'yan bindiga

A wannan karon ma dai budurwar ta sake bayyana a wani bidiyo inda ta yiwa mutanen da suke goyon bayana jarumi Ali Nuhu tatas, ga abinda Aisha ta ce a kasa:

"Assalamu Alaikum, me kike da suna 'yar gidan Ali Nuhu ko, Ali Nuhu ne yayi miki hanya kika samu shiga harkar fim, idan har Ali Nuhu yana son ya taimaka miki ba harkar fim zai sanyaki ba, zai biya miki kudi ne kije kiyi karatu kamar yadda yake biya 'ya'yansa. Saka ki a harkar fim da yayi ba gata bane yayi miki kansa ya yiwa, saboda yana samun kudi dake.

"Ba za ka taba ji yaran Ali Nuhu sun fito sunyi magana ba idan an taba addinin Musulunci, amma da an yi magana akan Ali Nuhu zasu fito su ishi mutane.

"Banyi niyyar yin magana ba, saboda ni ba 'yar zaman banza bace ina da abubuwan da nake so naga na zama a rayuwata."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel