Kungiyar manoma ta bayyana farashin da za ta dunga siyar da shinkafa daga yanzu

Kungiyar manoma ta bayyana farashin da za ta dunga siyar da shinkafa daga yanzu

A sakamakon yunkuri da gwamnatin tarayya ke yin a hana shigo da shinkafa yar kasar waje, kungiyar manoman shinkafar Najeriya ta ce, daga yanzu farashin buhun shinkafa ba zai haura 15,000 ba.

Shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Mohammed Abubakar Maifata, a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Alhamis, 29 ga watan Agusta a Abuja, ya bayyana cewa kungiyar za ta dauki mataki akan duk wanda aka samu yana sayar da buhun shinkafa sama da farashin kungiya.

A cewar Maifata, shinkafa yar gida da ake yi a Niaeriya ba ta wuce tsakanin naira 13,300 zuwa 14,000, yayin da ita kuma ta gwamnati ta kai 15,000.

Kungiyar ta bayyana cewa, ta aike wa gwamnatin tarayya wasika akan karya farashin shinkafa, domin ta karfafa mata wajen hana fasakaurin shinkafa a kasar nan.

Shuwagabannin kungiyar RIPAN sun bayyana cewa, Najeriya na asarar dala miliyan 400 wajen fasakaurin shinkafa daga kasar Jamhuriyar Benin.

Har ila yau Maifata tare da mataimakinsa Mista Paul Eluhaiwe sun bayyana cewa, sun kammala tuntubar mutanensu da ke bakin iyakar kasar.

KU KARANTA KUMA: Zaben sanata: Kotu ta soke karar da PDP ta shigar akan nasarar Al-Makura

Shugaban RIPAN din ya ci gaba da cewa, akwai tan 500,000 na shinkafa da ake kan hanyar shigo da su kasar nan daga Thailand kafin bikin kirsimeti.

A cewar shi, ba shakka wannan zai sa masu fasakaurin shinkafa su yi asarar dala miliyan 4000. A bangaransa, rufe iyakar da ke tsakanin Najeriya da kasar Benin zai taimaka wajen dakile fasakaurin shinkafa tare habbaka shinkafar gida.

Ya kara da cewa, kungiyar tana goyan bayan gwamnatin tarayya wajen kulle iyakar kasar nan. Kungiyar ta babbatar wa ‘yan Najeriya cewa, za ta saka wa ‘ya’yan kungiyar haraji domin ta cike gurbin farashin shinkafa a kasuwa, sakamakon rufe iyakar kasar.

Ta kara da cewa, kasar nan tana bukatar tan miliyan hudu na shinkafa a duk sheka, amma mambobin kungiyar za su shigo da shinkafa wanda ya kai tan miliyan biyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel