Sabuwar shekarar Musulunci 1441: Jahar Osun ta bayar da hutun aiki na kwana 1

Sabuwar shekarar Musulunci 1441: Jahar Osun ta bayar da hutun aiki na kwana 1

Gwamnan jahar Osun, Adegboyega Oyetola ya sanar da ranar Juma’a a matsayin ranar hutu ga ma’aikatan jahar don murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1441, inji rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnan ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Alhamuis, 29 ga watan Agusta, wanda ya yi daidai da 28 ga watan Zulhijja, daya samu sa hannun babban sakataren ma’aikatan cikin gida na jahar Osun, Adebisi Obawale.

KU KARANTA: Matsalar tsaro: Shehu Sani ya bayyana hanyar samun mafita ga gwamnonin Arewa

Gwamnan ya taya al’ummar Musulmai murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci, sa’annan ya yi kira ga Musulmai su dage da yi ma jahar Osun addu’o’in kariya, zaman lafiya, kwanciyar hankali, shugabanci nagari da samun cigaba mai daurewa.

“Yayin da muka shiga sabuwar shekarar Musulunci, ba wai kawai zamu yi ta murnar shiga bane, zamu zage damtse wajen bin umarnin Allah, ya zama dole mu dinga aiwatar da darussan dake tattare da Hijiran Annabi Muhammad (SAW) kamar su hakuri da juriya.

“Haka zalika gwamnatin na kira ga Musulmai da su kauce ma aikata manyan zunubbai da munanan dabi’u domin samun ingantaccen rayuwa a kansu, a jahar Osun da ma Najeriya gaba daya. Sa’annan kira ga dukkanin mabiya addinai daban daban dasu zauna da kowa lafiya ba tare da la’akari da bambancin addini ba.” Inji shi.

Ana sa ran shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1441 a ranar Asabar idan har an ga wata kamar yadda mai alfarma Sarkin Musulmi ya umarci Musulmai su fita neman watan, idan kuma ba’a ga watan ba, sabuwar shekara za ta fara ne a ranar Lahadi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng