Yanzu Yanzu: Hukumar NECO ta saki sakamakon jarrabawar Yuni/Yuli 2019
Hukumar jarrabawar kasa ta NECO ta saki sakamakon jarrabawar Yuni/Yuli 2019.
A bisa ga sakamakon da hukumar ta saki, dalibai 829,787 wanda ke daidai da kaso 71.59 cikin 100 sun samu kiredit biyar zuwa sama ciki harda harshen turanci wato Ingilishi (English) da kuma darasin lissafi (Mathematics).
Hakan na nufin an samu karuwa da kaso 0.11% idan aka kwatanta da sakamakon jarrabawar na Yuni/Yuli 2018.
A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto a baya cewa mai yiwuwa hukumar shirya jarrabawar shiga gaba da makarantun gaba da sakandire (JAMB) ta soke fiye da rabin sakamon jarrabawar da aka yi a shekarar 2019 a wasu jihohin kasar nan, kamar yadda wani ma'aikacin hukumar ya shaida wa majiyar mu.
KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun kama mutane 3 akan harin da aka kai wa motocin mataimakin gwamna
Jami'in, wanda ya nemi a sakaye sunansa, ya ce JAMB za ta soke sakamakon jarrabawar ne saboda magudin da aka tafka yayin rubuta jarrabawar da aka yi tsakanin 11 zuwa 18 ga watan Afrilu. Majiyar ta ce duk da an tafka magudi a kowanne bangare na Najeriya, lamarin ya fi muni a wasu jihohin.
Ya ce: "iyayen yara da masu cibiyar rubuta jarrabawa sun taimaka wajen magudin da aka tafka yayin jarrabawar, lamarin ya matukar bawa hukumar JAMB mamaki."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng