An kama mai sayar da kilishi da laifin zamba ta N2.2m a Legas

An kama mai sayar da kilishi da laifin zamba ta N2.2m a Legas

Son banza da son abin hannun wani da hausawa ke cewa shi ke sanya gidan yari cika, ya sanya a ranar Talata hukumar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Legas, ta samu nasarar cafke mutum dan shekaru 43 mai sana'ar sayar da kilishi.

Nnamdi Iloba ya shiga hannun hukumar 'yan sandan jihar Legas da laifin zambar dukiya ta hanyar karbar tilin nama na kimanin naira miliyan 2.2 wanda ya ce zai biya kudin bayan ya ci kasuwa.

An gurfanar da Nnamdi a gaban wata kotun majistire da ke zamanta a unguwar Ejigbo, inda ake zarginsa da laifuka biyu da na zambo cikin aminci da kuma yin handama da babakere kan dukiyar da ba ta sa ba.

Jami'in dan sanda mai shigar da kara a gaban kotu, ASP Kenneth Asibor, ya bayar da shaidarwa cewa, wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne tun a shekarar 2018 da ta gabata a yankin Isheri na jihar Legas.

Ya ce Nnamdi ya karbi bashin tulin nama na kilishi daga hannun wani abokin kasuwancinsa, Mista Reginald Nwobo, yayin da suka kulla yarjejeniyar zai biya kudin da zarar ya ci kasuwarsa, lamarin da ya sanya ya shafa wa idanunsa bakin kwalli da yin burus a zuwan ya ci banza.

KARANTA KUMA: EFCC ta cafke mutane 28 masu alaka da mazambata 77 da aka kama a Amurka

ASP Asibor ya ce laifin da Mista Nnamdi ya aikata ya saba wa sashe na 315 da kuma na 321 cikin kundin tsarin dokoki na jihar Legas da aka tanada tun a shekarar 2015.

A yayin dage sauraron karar zuwa ranar 16 ga watan Satumba, Alkalin kotun Mista T. O Shomade, ya bayar da umarnin garkame wanda ake zargi a gidan kaso, lamarin da ya ce zai nemi shawarar hukumar zartar da hukunci ta jihar.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel