Na gaji da zaman gida, Mourinho ya fadi abinda yafi bukata yanzu

Na gaji da zaman gida, Mourinho ya fadi abinda yafi bukata yanzu

Tsohon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Jose Mourinho, ya bayyana niyyarsa ta son sake koma wa aiki tare da bayyana cewa ya gaji da huta wa.

Tun bayan da kungiyar Manchester United ta sallame shi daga 'Old Trafford' mutane suka bayyana cewa Mourinho, wanda ya kasance mai horar wa a kungiyoyin nahiyar Turai da dama, ba zai iya dade wa ba tare da ya koma harkar wasan kwallon kafa ba.

Mourinho, dan asalin kasar Portugal, ya bayyana cewa yana kewar kwallon kafa tare da bayyana cewa a shirye yake ya kama aiki da duk kungiyar da ke sha'awar daukansa a matsayin horar wa.

Rahotanni sun bayyana cewa tsohon kociyan ya fi son ya samu aikin horar wa a daya daga cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa da ke kasar Ingila, Spain, Italy, Germany ko France.

DUBA WANNAN: Matar aure ta kashe mijinta saboda kawai ta koma gidan tsohon mijinta a Kebbi

A hirarsa da 'Sky Sports', Mourinho ya bayyana cewa: "na dauki tsawon lokaci ina tunani da nazarin abubuwa, amma yanzu a shirye nake domin koma wa filin daga.

"Abokaina na fada min cewa na more lokacina, haka suka fada min a watan Yuli da Agusta. Su hutu suke so min amma maganar gaskiya shine bana jin dadin wata rayuwa fiye da ta kwallon kafa, ba na jin dadin zama haka, zaman hutu. Na yi kewar kwallon kafa, kuma ina son koma wa filin wasa."

Sai dai, rahotanni da ke fitowa daga kasar Spain na nuni da cewa Mourinho na son dawowa kungiyar Real Madrid, ya na tunanin damar koma wa kungiyar kan iya samu wa kowanne lokaci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel