Da duminsa: Fadar shugaban kasa ta fitar da jawabi a kan labarin yi wa Buhari zanga-zanga a kasar Japan

Da duminsa: Fadar shugaban kasa ta fitar da jawabi a kan labarin yi wa Buhari zanga-zanga a kasar Japan

A cikin wasu takaitattun sakonni da ta wallafa a shafinta na dandalin sada zumunta (Twitter), fadar shugaban kasa ta yi kira ga 'yan Najeriya, a gida da ketare, da su yi watsi da wani labari mai dauke da bidyo da ke yawo a dandalin sada zumunta a kan cewa an kunyata shugaba Buhari da tawagarsa a kasar Japan.

"Mu na kira ga 'yan Najeriya a gida da ketare da su yi watsi da duk wani labari tare da faifan bidiyo da ke nuna zanga-zanga ko kunyata shugaban kasa tare da tawagarsa. Irin labaran nan ne da makiya ke yada wa, sai dai abinda basu sani ba shine tuni sauran 'yan Najeriya suka tafi suka barsu, an yi musu nisa.

"Shugaba Buhari zai gudanar da harkokinsa a wurin taron kasa da kasa a kan cigaban kasashen nahiyar Afrika (TICAD7) kum babu wani abu da zai dauke hankalinsa daga yin abinda ya kai shi wurin taron," a cewar jawabin mai dauke da sa hannun Femi Adesina, kakakin shugaban Buhari.

Da yammacin ranar Lahadi Legit.ng wallafa rahoton ta samu daga shafin mai taimaka wa shugaban kasa a bangaren kafafen sadarwa na zamani, Bashir Ahmad, da ya tabbatar cewa shugan kasa, Muhammadu Buhari, ya tashi zuwa kasar Japan.

DUBA WANNAN: Atiku ya 'fasa kwai' a kan dalilin da yasa Buhari ya fara binciken Obasanjo

A cikin sanarwar da Bashir ya fitar, ya bayyana cewa shugaba Buhari ya bar Abuja zuwa birnin Yokohama na kasar Japan domin wani halartar wani taron kasa da kasa da za a yi a ranar Laraba, 28 ga watan Agusta, 2019.

Za a yi taron ne a kan cigaban kasashen Afrika (CITAD), kuma wannan shine karo na bakwai da aka taba gudanar da taron tun da aka fara yinsa.

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, da takwaransa na jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu da kuma gwamnan jihar Kwara, Abdulrazak Abdulrahman, na daga cikin 'yan rakiyar shugaba Buhari zuwa taron na TICAD7.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel