Ana zaton wuta a makera: An kama Yansanda 3 da satar bindigogi

Ana zaton wuta a makera: An kama Yansanda 3 da satar bindigogi

Rundunar Yansandan Najeriya ta sanar da kama wasu jami’anta guda biyu da laifin satar bindiga kirar AK 47, guda biyu daga ma’ajiyar hukumar Yansanda, wanda kudinsa ya kai naira miliyan 1.7, inji rahoton jaridar The Nation.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito sunayen Yansandan kamar haka; Uzor Emmanuel mai shekara 34, Jimoh Halilu mai shekaru 27 da kuma Akharamen Michael dan shekara 31, wanda suke aikin tabbatar da tsaro na ‘Operation Wabaizigan’.

KU KARANTA: Da dumi dumi: El-Rufai zai fara biyan ma’aikatan Kaduna sabon albashi

An sace bindigun wadanda suke makare da harsashi ne daga hannun Michael da Jimoh a ranar 17 ga watan Yulin shekarar 2019 a wani gidan hutawa na Obodo dake titin Uwasota, unguwar Ugbowa cikin garin Bini, babban birnin jahar Edo.

Dansanda mai shigar da kara, Peter Ugumba da ya bayyana ma kotu cewa ana tuhumar Yansandan da laifukan da suka dangancin sata ne. inda yace Yansandan sun sace bindigun ne da nufin aikata laifin fashi da makami, garkuwa da mutane da kuma kashe kashen rayuka.

Dansandan Ugumba yace laifukan sun saba ma sashi na 390 (6) (9) na kundin hukunta manyan laifuka da kuma sashi na 3 (1) na dokokin hukunta laifukan fashi da makami da mallakan makamai na Najeriya.

Daga karshen zaman, Alkalin kotun ya umarci a garkame masa Yansandan 3 a gidan yari har sai ranar da za'a cigaba da zaman shari'ar.

A wani labarin kuma, wasu gungun yan bindiga sun kaddamar da hari a wani caji, watau ofishin rundunar Yansandan Najeriya dake Ikirike na jahar Enugu.

Wasu shaidun gani da ido sun bayyana cewa yan bindigan sun shiga ofishin Yansandan ne kamar za su kai musu kara, amma shigarsu ke da wuya, sai yan bindigan suka bude musu wuta.

Kaakakin rundunar Yansandan jahar Enugu, Ebere Amaraizu ya tabbatar da kai harin, amma yace babu wani mutu ko daya da aka kashe, amma yace sun kaddamar da farautar miyagun don hukuntasu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel