Da duminsa: Gwamna Wike ya yi magana a kan rushe Masallacin Juma'a a Ribas

Da duminsa: Gwamna Wike ya yi magana a kan rushe Masallacin Juma'a a Ribas

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi Alla-wadai da labaran da ya kira na 'karya' da ake yada wa a wasu kafafen yada labarai da dandalin sada zumunta a kan cewa gwamnatin jiharsa ta rushe wani Masallaci a garin Fatakwal, babban birnin jihar Ribas.

Wike ya bayyana masu yada labarin a matsayin makiya jihar Ribas da ke burin son haddasa fitina a tsakanin al'umma.

Da yake ganawa da manema labarai a kan titin Biambo dake kusa da kwanar tsohuwar kasuwar Mami, wurin da aka ce an rushe masallacin, Wike ya ce babu wani ginin Masallaci a wurin, a saboda haka ba a rushe komai ba a wurin.

"Manyan mutane a fadin kasar nan sun kira ni a kan labarin rushe Masallaci a Fatakwal da ke yawo a yanar gizo. Shi yasa na zo har wurin da 'yan jarida domin su ga wurin, su san cewa babu wani Masallaci a wurin.

"Abin bakin ciki ne a ce wasu mutane, da babu alheri a cikin zuciyarsu, suna yada cewa an rushe Masallaci a wannan wurin, yayin da babu wani gini ma a wurin. Wasu makiya jihar Ribas ne ke yada labarin domin cimma muguwar manufarsu," a cewar Wike.

DUBA WANNAN: Jirgin sama ya yi saukar gaggawa bayan direba ya suma

Gwamna Wike ya bayyana cewa gwamnati ta sa an baje wurin ne bayan wasu mutane sun fara gini ba tare da izini ba.

"Sun zo sun fara gini ba tare da samun sahalewar hukuma ba. Gwamnatin jihar Ribas ba ta bawa kowa izinin yin gini a wurin ba.

"Mutanen da suka zo suka fara gini a wannan wuri tuni suka garzaya kotu a kan maganar filin wurin, kuma gwamnatin jihar Ribas ce ta samu nasara a kotun. Amma duk da haka suka fara gini a wurin domin kawai su jazawa gwamnatin jihar Ribas bakin jini," a cewarsa.

Gwamnan ya kalubalanci Musulman jihar Ribas da su nuna wurin da gwamnati ta rushe musu Masallaci tare da basu shawarar cewa kar su bari a yi amfani da su domin dalilan siyasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel