Ango da Amarya sun mutu mintuna kadan bayan kammala daurin aurensu

Ango da Amarya sun mutu mintuna kadan bayan kammala daurin aurensu

- Wasu tsofaffin masoya da suka jima suna mafarkin yin aure sun rasa rayukansu mintuna kadan bayan daurin aurensu

- An bayyana cewa masoyan sun fara soyayya tun suna 'yan shekara 13 a duniya, inda kullum maganarsu ita ce yadda za ayi suyi aure tare

- Lamarin dai ya faru ne a daidai lokacin da angon da amaryar suke kokarin fitowa daga wajen daurin auren a motarsu, inda suka yi taho mu hadu da wata katuwar mota

Ango da amarya sun rasa rayukansu yayin wani hatsari da ya rutsa dasu, mintuna kadan bayyan kammala daurin aurensu.

Harley Joe Morgan mai shekaru 19 da angonta Rhiannon Boudreaux Morgan mai shekaru 20, sun amince da zama mata da miji, a daidai lokacin da suke shirin fita daga wajen daurin auren nasu suka yi taho mu gama da wata katuwar mota.

Angon yana tuka wata farar mota kirar Chevrolet yayin da suka hadu da wata katuwar mota da misalin karfe 3 na ranar Juma'ar nan da ta gabata.

KU KARANTA: Akwai 'yan Boko Haram a kowacce kabila ta kasar nan - Gwamnan Borno

Angon da amaryar, wanda suke 'yan garin Orange County, an bayyana mutuwarsu a take a wajen da hatsarin ya faru. Sai dai kuma direban babbar motar ko kwarzane bai yi ba, in ji hukumar 'yan sandan jihar.

Harley da Rhiannon masoya ne tun suna yara, kuma kullum babban burinsu shine su yi aure tare.

Mahaifiyar Harle, Lashawna Morgan da kanwarta lamarin ya faru a kan idonsu ne, a daidai lokacin da suke bin motar amaren a baya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel