Na girgiza a kan rashin ganin suna na cikin ministocin Buhari – Tsohon minista

Na girgiza a kan rashin ganin suna na cikin ministocin Buhari – Tsohon minista

-Tsohon ministan sadarwa Adebayo Shittu ya ce yayi mamakin rashin fitowar sunansa cikin ministocin Buhari

-Shittu ya kara da cewa wannan abu da ya faru ba komai bane illa kaddara a matsayinsa na musulmi kuwa ya yi imani da ita

Adebayo Shittu, tsohon ministan sadarwa ya ce ya girgiza matuka bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya fitar da sunayen ministoci ya ga babu sunansa a ciki.

Shittu yayi wannan jawabin ga kamfanin dillacin labaran Najeriya NAN a Abuja, inda ya ce duk da cewa bai yi tsammanin za a fitar da sunayen ministoci babu nasa amma dai a matsayinsa na musulmi ya rungumi kaddara.

KU KARANTA:Rashin tsaro: Hare-haren da suka auku cikin makon da ya gabata a Najeriya

Tsohon ministan ya ce: “Na karbi wannan abin a yadda ya zo mani.” NAN ruwaito mana cewa a ranar 23 ga watan Yuli Shugaban Majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan ya karanto sunayen mutum 43 da Shugaba Buhari ya zaba a matsayin ministoci.

A cikinsu akwai 14 wadanda tsoffin ministoci ne yayin da 29 kuma sabbi wadanda a karon farko kenan da za su rike irin wannan mukamin a karkashin mulkin Buhari.

“Ko shakka babu ban taba tunanin suna na ba zai fito cikin ministocin da za nada ba, amma kuma a matsayina na musulmi cikin minti biyar na mika lamarina ga Allah na rungumi kaddara.

“Haka Allah ya tsara mani, na kuma yi kokarin tuna wata aya cikin Al-kur’ani wadda ke magana a kan so tari zaka so ya kasance bai alkhairi bane a gareka.

“A don haka ni tuni na mika al’amarin ga Allah na san ya yi mani wani tanadin na daban kuma wanda ma ya fi wannan alkhairi. Allah ya san dalilin da ya sa suna na bai fito cikin ministocin ba.” Inji Shittu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel