Gwamnan jihar Borno ya gana da shugaba Buhari

Gwamnan jihar Borno ya gana da shugaba Buhari

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum a ranar Juma’a, 23 ga watan Agusta, ya yi ganawa na musamman da shugaban kasa Muhammadu Buhari akan hare-haren da yan ta’addan Boko Haram suka kai kananan hukumomin Gubio, Magumeri da Konduga dake jihar a wannan makon.

Hadimin gwamnan, Malam Isa Gusau yace sun yi ganawar ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja bayan sallar Juma’a.

A yayin tattaunawar, kakakin gwamnan ya bayyana cewa Gwamna Zulum ya koro jawabai akan tsaro bayan hare-haren da yan ta’addan suka kai a daren ranar Laraba, a yankunan kananan hukumomin Gubio da Magumeri hade da hare-haren da suka kai a ranar Alhamis a kauyukan Wanori, Kalari da Dori duk a karkashin Konduga.

Gusau ya kara da cewa Gwamna Zulum ya yi sharhi akan lamarin tsaro musamman a yankin Arewacin Borno inda aka fi kai hare-hare.

Ya bayyana cewa saduwa da shugaban kasar ya bayyana matakan da gwamnatin tarayya ta shirya tare da tabbacin cigaba da karfafa kokari don ganin an samar da zaman lafiya da daidaituwa a jihar Borno da sauran yankunan Arewa maso gabas.

Ya bayyana cewa a ganawa da shugaban kasar ya bayyana matakan da gwamnatin tarayya ta dauka tare da tabbacin ci gaba da karfafa kokarin da ake, wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Borno da sauran yankin arewa maso gabas.

Gwamna Zulum wanda ya bar fadar shugaban kasa da misalin karfe 4 na rana inda ya zanta da mataimakin shugaban kasa akan batun.

KU KARANTA KUMA: Jerin sunayen Yan Najeriya 80 da aka kama da zambar miliyoyin daloli a kasar Amurka

Ku tuna a baya cewa gwamnan ya tafi Gubio a ranar 11 da 14 ga watan Agusta bisa al’amuran da suka shafi tsaro.

Yayin ziyaran ne Gwamna Zulum ya sadu da kwamandan Operation Lafiya Dole na lokacin, Major General Manjo Janar Benson Akinroluyo da kwamandan 5 brigades wanda ke kulawa da Gubio inda rundunar sojin ta ba da tabbacin ci gaba da tallafa ma yankin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel