Wadume: 'Yan sanda sun kama Shugaban APGA da wasu mutum 7

Wadume: 'Yan sanda sun kama Shugaban APGA da wasu mutum 7

Rundunar 'Yan sandan Najeriya ta kama shugaban jam'iyyar All Progressives Grand Alliance, APGA, na karamar hukumar Ibbi tare da wasu mutane bakwai ciki har da malamin addinin musulunci game da binciken da ake gudanarwa kan gawurataccen mai garkuwa da mutane, Hamisu Wadume.

Shugaban na jam'iyyar APGA da aka ce abokin Wadume ne ya jagorancin sauran mutanen bakwai daga karamar hukumar Ibbi da malamin addinin musuluncin zuwa wurin DCP Abba Kyari kan binciken Wadume.

Daily Trust ta gano cewa Abba Kyari ya bayar da umurnin tsare shugaban na APGA da mutane bakwai din ne saboda samunsu da yunkurin neman a sako Wadume.

DUBA WANNAN: Kotu: Ganduje ya gabatar da shaida mai katin zabe na bogi

Wata majiya ta ce Kyari da sauran 'yan kwamitin binciken suna nan a garin suna tattara bayanai kan lamarin. Majiyar ta kara da cewa Kyari ya shaidawa Sarkin Ibbi cewa mutanen garin da ba su da hannu cikin aikata laifi ba su kwantar da hankulan su yayin wani taro da su kayi.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa mazauna garin sun ce yanzu kwanaki 14 kenan ba a samu labarin sace mutane ba a garin tun bayan kama Wadume. Daya daga cikin majiyar, Nuhu Noka ya shaida wa majiyar Legit.ng cewa kusan kullum sai an sace mutane a hanyar Wukari zuwa Takum amma a yanzu makonni biyu hanyar lafiya kalau.

Ya ce an sako wasu mutane hudu da aka sace aka tsare su a wani wuri kusa da Kofan Amadu a hanyar Takum zuwa Wukari bayan kimani watanni biyu suna da sace su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel