Tirkashi: Lokacin ina 'yar shekara takwas a duniya sai da kanin Kakana yayi lalata dani - Juliet Ibrahim

Tirkashi: Lokacin ina 'yar shekara takwas a duniya sai da kanin Kakana yayi lalata dani - Juliet Ibrahim

- Fitacciyar jarumar nan 'yar kasar Ghana ta bayyana cewa lokacin da tana 'yar shekara takwas a duniya sai da aka yi lalata da ita

- Ta ce kuma lokacin da tana 'yar shekara 18 taki amincewa ta auri wani bature saboda irin kokarin da take yi a wancan lokacin na ganin ta zama jarumar fim

- Ta ce a cikin mutanen da suka yi mata fyaden akwai kanin kakanta, 'yan uwanta da kuma wani abokinta

Fitacciyar jarumar nan ta Nollywood 'yar kasar Ghana Juliet Ibrahim ta bayyana cewa kanin kakanta ya taba yi mata fyade lokacin da tana 'yar shekara takwas a duniya, jarumar ta bayyana hakan ne a lokacin da take bayani da manema labarai a lokacin gabatar da wani littafinta mai suna 'A Toast to Life'.

Fitacciyar jarumar 'yar kasar Ghana a cikin hirar tata da gidan rediyon Cool FM, ta bayyana cewa irin soyayyar da take yiwa 'yan fim da kuma kokarinta na ganin ta zama jarumar fim yasa taki yadda wani bature ya aureta lokacin da tana shekara 18. A cewarta mutumin ya daina kiranta ya kuma daina taimakawa iyayenta bayan taki amincewa ta aureshi.

KU KARANTA: Iko sai Allah: Tsananin soyayyar da mijinta yake nuna mata yasa wata Balarabiya neman kotu ta raba aurensu da mijin nata

Juliet ta kuma yi magana akan fyade da aka yi mata sau hudu lokacin tana 'yar shekara takwas a duniya wanda har yau baza ta taba mantawa da shi ba.

A cewar jarumar wacce take da da guda daya, ta ce kanin kakanta ya taba yi mata fyade, daga shi kuma sai wasu 'yan uwanta sai kuma wani abokinta shima yayi mata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel