Iko sai Allah: Tsananin soyayyar da mijinta yake nuna mata yasa wata Balarabiya neman kotu ta raba aurensu da mijin nata

Iko sai Allah: Tsananin soyayyar da mijinta yake nuna mata yasa wata Balarabiya neman kotu ta raba aurensu da mijin nata

- Yayin da wasu matan ke neman irin wannan mijin ruwa a jallo, ita kuma taje kotu ta raba aurensu saboda soyayyar da yake nuna mata

- Matar wacce ke zaune a kasar Dubai ta kaiwa kotu wannan kara ne domin ta raba aurensu inda ta bayyana cewa mijintan yana nuna mata soyayyar da ta wuce iyaka

- Ta ce lokuta da dama yana tashi ya gyara mata gida ba tare da ta ce yayi ba, ko kuma ya siyo mata kyautuka masu yawa ya kawo mata

Wata mata dake zaune a hadaddiyar daular Larabawa ta nemi a raba aurenta da mijinta saboda yana nuna mata soyayyar da ta wuce misali, wajen tayata aikin gida da kuma bata kyaututtuka masu yawa.

Matar ta nemi a raba auren nasu ne a wata kotun Shari'ar dake Fujairah, inda ta ce soyayyar mutumin ta yi matukar kamata. Mijin nata yana da kirki sosai da ya wuce misali.

KU KARANTA: Jarumai goma da suka fi kowa kudi a masana'antar Kannywood

"Ina matukar kaunar shi, yana da kirki sosai, yana taimaka mini wajen ayyukan gida ba tare dana ce yayi ba. Ina so na samu koda rana daya ce tawa ta kaina, amma hakan ba zai yiwu ba idan har mijina wanda koda yaushe yake nuna mini kulawa da bani kyautuka masu yawa a koda yaushe."

Jaridar Khaleej Times ta ruwaito cewa mijin ya roko kotu akan kada ta yarda da abinda matar take rokonta da tayi. Ya ce yana mamaki yadda aka yi matarsa take son rabuwa da shi.

A karshe dai kotu ta daga sauraron karar domin ta bai wa ma'auratan dama su sasanta junansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel