Tirkashi: Aisha Idris ta fara tona asiri gami da bayyana sakonnin sirri da Afakallahu ya aikata mata

Tirkashi: Aisha Idris ta fara tona asiri gami da bayyana sakonnin sirri da Afakallahu ya aikata mata

- Bayan bayyana a wani bidiyo da tayi kwanakin da suka gabata inda take ciwa shugaban tace fina-finai na jihar Kano, akan cewa dan iska ne

- Yanzu haka budurwar ta fara sakin wasu bayanin sirri na sakonni da shugaban 'yan fim din ya aika mata a shafinta na Instagram

- Sannan kuma ta bayyana cewa akwai sauran wasu bayanan wanda za ta aiko nan ba da dadewa ba

Bayan kama darakta Sunusi Oscar da hukumar tace fina-finai tayi a makon da ya gabata, wata budurwa mai suna Aisha Idris ta fito ta yiwa shugaban hukumar wankin babban bargi, a cewar ta shima ba mutum ne na gari ba, har ta bayyana cewa ya sha yi mata magana ta sirri a shafin sadarwa na Instagram, inda kuma ta sha alwashin za ta bayyana.

Bayan maganganun na ta Aisha tasha martani da zage-zage daga magoya bayan shugaban, inda har Jarumi Aminu Ahlan ya bayyana cewa dama can karuwa ce ita aka dauki nauyinta don ta ci zarafin Afakallahu.

Kwatsam sai jiya Aisha ta fara wallafa wata hira da ta gudana tsakaninta da wani mai shafin Instagram da suna Isma'il Na Abba Afakallahu mai dauke da hoton fuskar gwamnan Kano wanda babu tabbacin shafin na Afakallahu ne, ko kuma wanine ke amfani da sunansa kamar yadda aka sha yiwa mashahuran mutanen sojan gona.

KU KARANTA: Sanata Abbo ya kai karar mutumin da ya kirashi da mai Kanjamau, Dan Luwadi, Dan Giya sannan kuma mai neman mata

Duk da dai hirar ta su babu wata magana ta banza da ta shiga tsakaninsu, amma ya tambayeta inda take tayi masa bayani da cewa ita 'yar Najeriya ce daga jihar Borno amma tana zaune a kasar Jamus, sannan shi kuma ya ce mata shi dan Kano ne inda har ya aikata mata da lambar wayarshi.

Sai dai Aisha ta bayyana cewa wannan kadanne, ma'ana akwai sauran magana da sai nan gaba zata fito, kana ta sake wallafa wani bidiyo, inda ta cigaba da caccakar Afakallahu da masu yi mata martani a madadinsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel