Kotu: Ganduje ya gabatar da shaida mai katin zabe na bogi

Kotu: Ganduje ya gabatar da shaida mai katin zabe na bogi

Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano na Jam'iyyar APC ya fara kare kansa a gaban kotun sauraron karar zaben gwamna a jihar Kano inda ya gabatar da shaidan baka da wasu takardu sai dai an gano shaidan yana dauke da katin zabe na bogi ne.

Idan ba a manta ba kotun na sauraron karar da jam'iyyar PDP da dan takarar gwamnan ta Abba Kabir Yusuf ya shigar ne na kallubalantar nasarar Ganduje a zaben gwamna da aka gudanar a Maris din 2019.

Yayin sauraron shari'ar, jagoran lauyoyin Ganduje, Ofiong Ofiong, SAN, ya gabatarwa kotu hujjoji na takardun sakamakon zabe (fom EC8A) daga kanananan hukumomi 28 inda aka gudanar da zaben raba gardama.

Sauran hujjojin da ya gabatar sun hada da ainihin kofi na fom EC40G da kofi na rahoton zaben ranar daga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, INEC.

DUBA WANNAN: Zanga-zangar juyun juya hali: Kungiyoyin Arewa 9 sun tsame hannunsu, sun bayar da dalili

Wadanda akayi karar sun kuma gabatar da shaidun baka uku daga mazabar Gawa da ke karamar hukumar Nasarawa a jihar.

Shaidan na farko, Abubakar Suleiman mazaunin Kasuwar Murtala daga mazabar Gama D, a karamar hukumar Nasarawa ya yi ikirarin cewa a zaben ranar 9 ga watan Maris, wasu magoya bayan PDP a akwatin zabensa sun mika sunayen wasu mutane 20 ga jami'an INEC kuma suke hakikance dole sai sun fara yin zabe kafin wani ya jefa.

Yayin da ya ke amsa tambayoyi, Suleiman ya tabbatar da cewa wani mutum da bai sani ba ne ya rattaba hannu kan sakamakon zaben a madadin PDP yayin da wasu Auwalu ya rattaba hannu a madadin APC.

Sai dai abin mamaki a lokacin da aka bukaci Suleiman ya gabatar da katin zabensa, sai aka gano katin na dauke da sunan Sadiq Sadiq. Hakan ya sa lauyan PDP Eyitayo Fatogun tafka mahawara mai zafi da lauyan Ganduje, MN Duru kan batun.

Daga bisani lauyoyin na Ganduje sun gabatar da sauran shaidunsu biyu, inda daya daga cikinsu ya yi ikirarin cewa wasu matasa kimanin 20 da ya yi ikirarin ba su kai shekarun zabe ba sun jefa kuri'a a akwatinsa da ke Layin Maigado sai dai ya gaza bayyana tabbas din cewa ba su isa zaben ba illa kawai ya ce suna sanye da jar hula wadda kotun ta ce ba takamamen hujja bane da ke nuna jam'iyyar da suke goyon bayan.

Daga karshe dai daya daga cikin lauyoyin wadanda akayi kara, Aliyu Umar, SAN, ya bukaci kotu da dage sauraron karar zuwa ranar Juma'a 23 ga watan Augustan 2019 kuma Alkalin kotun ta amince da hakan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel