Wata shari’ar sai a lahira: Yadda Boko Haram ke daura ‘aure kan aure’

Wata shari’ar sai a lahira: Yadda Boko Haram ke daura ‘aure kan aure’

A duk lokacin da kungiyar ta’addanci ta Boko Haram ta kama wani gari a yankin Arewa maso gabashin Najeriya, abinda take yi shine kakabawa tare da dabbaka dokokinta a kan jama’an da suka rage a garin, bayan sun kashe na kashewa, masu gudu sun gudu.

Wani bincike da jaridar Daily Trust ta gudanar ya nuna cewa Boko Haram na daura aure a kan aure a tsakanin mutanen da suka kama, ma’ana idan matar wani ta tsere, ko kuma mijin wata ya tsere, sai ta hadasu aure ba tare da la’akari akwai igiyar aure a kanta ba.

KU KARANTA: Za mu dauki yan bautan kasa da yan N-Power aikin tsaro – Gwamnatin FG

Wata shari’ar sai a lahira: Yadda Boko Haram ke daura ‘aure kan aure’
Falmata da Usman
Asali: Facebook

Majiyar Legit.ng ta ruwaito tabbas wannan ya saba ma shari’ar addinin Musulunci, amma a irin addinin Boko Haram, duk wanda ya tsere daga hare harensu ya zama kafiri, don haka dole su rabashi da matarsa ko mijinta kamar yadda suka rabashi da addinin.

Sai dai shuwagabannin gargajiy a garuruwan da irin wannan jagwalgwalo ke aukuwa suna kokarin kashe ire iren haramtattun auren nan da zarar an gano inda miji ko matar da ta tsere suke, sai dai duk haka aikin gama ya gama, saboda tun kafin lokacin wasu ma’auratan har sun tara da juna.

Majiyarmu ta hadu da wata mata mai suna Falmata Usman, wanda mijinta Usman Modu ya tsere zuwa kamaru daga kauyen Dugje dake cikin karamar hukumar Bama yayin da Boko Haram suka shiga garin, sai Boko Haram ta aurar da Falmata ga wani mutumi da suka kama a garin, Adam Ali, wanda shi kuma matansa 2 suka tsere.

Amma cikin ikon Allah sai Falmata da mazajen nata biyu, Usman da Adam sun hadu a sansanin yan gudun hijira dake Bama, nan take dakaci Bulama Ashemi ya kashe sabon auren da Boko Haram ta daura mata da Adam, kuma ta koma ga mijinta Usman.

An samu saukin warware wannan haramtaccen aure hadin Boko Haram ne da taimakon kungiyoyi masu zaman kansu kamar Internationa Alert da kuma Herwa Initiatives. Allah Ya shiryar damu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel