Sarkin Zazzau ya gabatar da bukatar Zazzagawa ta musamman ga Buhari
- Ma Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris ya roki Shugaba Buhari ya ceto Asibitin Koyarwa na Jami'ar Ahmadu Bello (ABUTH)
- Sarkin ya kuma bukaci Shugaban kasar ya taimaka wurin ganin an farfado da masana'antun da suka durkushe a Jihar
- Harwayau, ya roki Shugaba Muhammadu Buhari ya taimaka wurin sake gina wasu muhimman tittuna a jihar ta Kaduna
Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris a ranar Alhamis ya bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taimaka wurin magance kallubalen da ke hanna Asibitin Koyarwa ta Ahmadu Bello ABUTH da ke Zaria gudanar da ayyukanta kamar yadda suka dace.
Alhaji idris ya yi wannan kirar ne yayin da ya ke tarbar shugaban kasar da ya kai masa ziyarar ban girma a fadarsa da ke Zaria a hanyarsa ta zuwa kaddamar da aikin ruwa na Zaria da gwamnatin Kaduna da hadin gwiwan wasu suka kammala.
DUBA WANNAN: Da duminsa: Buhari da El-Rufai sun ziyarci fadar Sarkin Zazzau (Hotuna)
Sarkin ya ce: "ABUTH tana daya daga cikin tsaffin asibitocin koyarwa a kasar nan kuma tana da kwarrarun ma'aikata. Amma rashin isasun kudade da sauran kayan aiki na kawo cikas ga asibitin. A kan hakan ne na ke rokon mai girma ya saka baki a batun."
A kan kaddamar da aikin ruwan kuma, Alhaji Idris ya ce ya yi imanin cewa batun matsalar ruwa a Zaria zai zama tarihi. Ya shawarci shugabanni su zama masu hangen nesa musamman wurin samar da tsaro da rage talauci.
Alhaji Idris ya kuma bukaci Shugaban kasar ya bayar da muhimmanci wurin farfado da masana'antun da suka durkushe a Kaduna tare da sake gina tittunan Zaria-Pambegua, Kaduna-Jos da Zaria-Funtua.
A bangarensa, Buhari ya tabbatarwa Sarkin cewa gwamnatinsa ba za tayi kasa a gwiwa ba wurin magance kallubalen tattalin arziki da tsaro da kasar ke fuskanta kamar yadda ya yi alkawari yayin yakin neman zabensa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng