Shehu Hassan Kano ya zama limamin daidaita sahun kungiyar Kannywood

Shehu Hassan Kano ya zama limamin daidaita sahun kungiyar Kannywood

- Hukumar tace fina-finai ta kasa ta sanya jarumi Shehu Hassan Kano a matsayin wanda zai jagoranci tantance 'yan wasan Hausa na kungiyar Kannywood

- Kwamitin za ta fara aikin tantancewar ne ranar Litinin dinnan mai zuwa, sannan abin zai dauki tsawon wata guda ana yin shi

- Tantancewar za ta shafi marubuta, masu daukar hoto, masu tace hoto, masu shiryawa, masu bayar da umarni da dai sauransu

Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano karkashin jagorancin shugabanta Isma'il Afakallahu ya rantsar da kwamitin tsoffin 'yan fim da zasu tantance duk masu ruwa da tsaki a harkar fim din Hausa.

Kwamitin da Shehu Hassan Kano ke jagoranta zai fara aikin tantancewar ne ranar Litinin mai Zuwa zai kuma dauki tsawon wata guda yana aikin tantancewar.

A tattaunawar da yayi da manema labarai Shehu Hassan Kano ya bayyana manufar kwamitin shine tsaftace harkar fim din Hausa da marasa manufa da tarbiyya da suka cika kungiyar da badala maimakon basira da gogewa.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Kwallon kafa halak ne a Musulunci - Sheikh Ibrahim Khalil Kano

Ya kuma jaddada kudirinsu na cewar ana son samar da nagartattun masana ne harkar domin dawo da martabar masana'antar kamar yadda take a baya.

Sannan kuma za a rage kwaranyowar mata 'yan kama waje-zauna da suka mamaye harkar fim ba tare da sun zo da muharramansu su ba. Hakazalika kwamitin zai rika ladabtar da masu zagi gami da batanci a kafar sadarwa.

Tantancewar za ta shafi marubuta, masu daukar hoto, masu tace hoto, masu shiryawa, masu bayar da umarni, mawaka da makada, masu daukar nauyi, masu kwalliya da sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel