Ganduje vs Abba Gida-Gida: Kotu ta bayar da umurnin kamo wadanda suka kaiwa shaidan INEC hari

Ganduje vs Abba Gida-Gida: Kotu ta bayar da umurnin kamo wadanda suka kaiwa shaidan INEC hari

Kotun sauraron karrar zabe na gwamnan Kano, karkashin jagorancin Justice Halima Shamaki ta bayar da umurnin kamo wadanda ake zargi da kaiwa wata ma'aikaciyar INEC, Halima Sambo Hassan da ta bayar da shaida a kan shari'ar zaben gwamnan Kano da ke gaban kotun.

Alkalin ta bayyana harin da aka kaiwa Hassan a matsayin 'gidadanci' kuma ta bawa hukumomin tsaro umurnin fara bincike kan lamarin. Ta kuma bukaci jami'an tsaron su binciko wadanda suka kai harin tare da hukunta su kamar yadda doka ya tanada.

Justice Shamaki ta ce kotun ba za ta amince da duk wani rashin da'a daga magoya bayan jam'iyyun da suka shigar da kara a kotun ba.

DUBA WANNAN: Sunaye da mukami: Buhari ya yi wasu sabbin muhimman nade-nade a ofishin Osinbajo

Ta yi gargadin cewa, "Idan har anyi barazana ga rayuwar shaidu, babu yadda zamu zauna mu nade hannu kamar babu matsala."

Alkaliyar kotun ta ce akwai wasikar da aka rubuto mata ne neman mayar da shari'ar zuwa Abuja domin babu 'cikaken tsaro a Kano'.

Lauya mai kare INEC, Adedayo Adedeji ya sanar da kotun cewa an yi wa Halima wacce da bayar da shaida a gaban kotun barazana daban-daban.

Adedeji ya yi ikirarin cewa ana ta yada hotunan shaidan a kafafen intanet tare da barazana ga rayuwar ta da kalamai na cin mutunci.

Ya roki kotun ta hana magoya bayan jam'iyyu hallartar zaman sauraron shari'ar muddin ba a dena yi wa shaida barazana ba.

Jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) reshen jihar Kano tayi tir da cin mutunci da barazanar kisa da aka yi wa mai bayar da shaidan. Lauya mai kare dan takarar gwamnan PDP, Abba Kabiru Yusuf, Maliki Kuliya Umar ya yi Allah wadai da hare-haren da aka kaiwa shaidan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel